Da Dumi-Dumi: Wasu mutane a Keke Napep sun yi awon gaba da yara yan shekara 4 a Legas

Da Dumi-Dumi: Wasu mutane a Keke Napep sun yi awon gaba da yara yan shekara 4 a Legas

  • Wani mutumi da ba'a san manufarsa ba ya yaudari kananan yara biyu, ya yi awon gaba da su a Keke Napep a jihar Legas
  • Mahaifiyar ɗaya da cikin kananan yaran da ba su wuce shekara 4 ba, ta ce bayan sun dawo daga makaranta suka fita wasa
  • Hukumar yan sanda reshen jihar Legas, ta ce tuni ta umarci jami'anta su bazama neman mutumin domin kubutar da yaran

Lagos - An sace wasu kananan yara guda biyu, Wasiu Dauda da Al-Ameen Ibrahim, a yankin Ijesha dake jihar Legas.

Daily Trust ta rahoto cewa kananan yara, dukkan su ba su wuce shekara huɗu ba, sun bata ne da misalin ƙarfe 4:00 na yammacin ranar Jumu'a bayan sun dawo daga makaranta.

Bayanai sun nuna cewa Wasu mutane ne suka ɗauke su a Keke Napep suka yi awon gaba da su yayin da suke wasa a yankin Anguwar da suke zaune.

Kara karanta wannan

Jirgin kasan Legas zuwa Ibadan ya tsaya tsakiyar daji saboda mai ya kare

Jihar Legas
Da Dumi-Dumi: Wasu mutane a Keke Napep sun yi awon gaba da yara yan shekara 4 a Legas Hoto: channelstv.com
Asali: UGC

Wannan na zuwa ne awanni kaɗan bayan an kama wani ɗan saƙo a Legas ɗin ɗauke da jariri a cikin akwatin dako.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Kazalika a kwanakin baya da suka gabata aka gano gawar wata Fasinja da ta ɓata bayan siyan tikitin tafiya a tashar motar BRT duk a jihar Legas.

Wane mataki iyayen yaran suka ɗauka?

Mahaifiyar ɗaya daga cikin yaran da aka sace, Awawu, wacce ta tabbatar wa manema labarai da faruwar lamarin, tace tuni suka kai rahoto ofishin yan sanda dake Ijesha.

Ta ce babban cikinsu, Sunday ɗan shekara 10, ya faɗa musu cewa wani mutumi ne ya ɗauke su da nufin zai siya musu wasu kyautuka na yara.

Awawau ta ce:

"Yaran sun dawo makaranta wajen karfe 2:00 na ranar Jumu'a. Bayan sun ci abinci suka kama gabansu. Da na tambayi Sunday bayan ɗan wani lokaci sai ya faɗa mun ya barsu suna wasa."

Kara karanta wannan

Gudun tsira: Mutune sun mutu garin gudun tsira a wani kauyen Katsina

"Bayan mintuna 30 sai babar Al-Ameen ta zo tana nemansa, na faɗa mata zasu dawo nan da anjima. Bayan rabin awa na fara shiga damuwa, ba Wasi'u ba labarinsa."
"Sunday ya gaya mana wani mutumi ya nemi mu bi shi ya siya mana Biskit amma ni kam na ƙi zuwa. Wani mai siyar da kayan tsotse-tsotse ne ya gaya mana ya ga lokacin da aka saka su a Keke Napep."

Wane mataki yan sanda suka ɗauka?

Kakakin hukumar yan sanda na jihar, CSP Adekunle Ajisebutu, ya sanar da cewa tuni aka ta da tawagar jami'an tsaro domin binciko yaran.

A wani labarin kuma Wani mutumin Kano ya fara tattaki daga Abuja zuwa Legas don goyon bayan Tinubu ya gaji Buhari a 2023

Wani mutumi ɗan asalin jihar Kano ya kuduri aniyar yin tattaki tun daga Abuja zuwa Legas domin nuna wa Tinubu ana tare.

Hussein Lawan ya ce zai yi wannan sadaukarwa ne a madadin matasa ya roki Tinubu ya fito takara don tallafawa matasa.

Kara karanta wannan

Indiya ta maye gurbin Najeriya matsayin hedkwatar talauci na duniya

Asali: Legit.ng

Online view pixel