Zanyi tsirara: Banki sun ciri kudin wata mata, ta haukace musu akan N100k

Zanyi tsirara: Banki sun ciri kudin wata mata, ta haukace musu akan N100k

  • Fiye da mintuna 34, an hargitsa zaman lafiya da ayyukan banki a wani banki yayin da wata mata ta fusata ta nuna rashin jin dadin ta cikin wani yanayi
  • Matar ta nadi bidiyo kai tsaye yayin da ta hana ma’aikatan banki sauraran kwastomomi kan cire mata N100k da aka yi a asusunta
  • Kokarin da ma’aikatan banki da jami’an tsaro da wasu kwastomomi suka yi na kwantar da hankalin matar ya ci tura yayin da ta yi barazanar za ta yi tsirara

An sha dirama a zauren banki yayin da wata 'babban mata' ta tada hankali banki a kokarinta na ganin an warware matsalarta.

Matar ta dauki lamarin a hannunta ta hanyar hana ma'aikatan banki sauraran sauran kwastomomi a cikin bankin.

Matar da ta haukacewa banki saboda N100K
Zanyi tsirara: Banki sun ciri kudin wata mata, ta haukace musu akan N100k | Hoto: Hammid Bakare
Asali: Facebook

A cikin wani bidiyo kai tsaye da ta dauka, kamar yadda wani a Facebook Hammid Bakare ya yada, matar ta koka kan yadda aka cire mata N100k a asusunta, kuma ta je bankin tsawon wata daya amma ba a biya mata bukata ba.

Kara karanta wannan

Maryam Booth: Na gaji da amsa tambayar yaushe zanyi aure da me yasa na rame

Matar da ta nuna bacin ranta ta bayyana cewa a maimakon a biya mata bukata, ma’aikatan bankin sun saka ta sawu-sawu a bankin tare da daurata kan hanyoyin da ba su kawo wani sakamako mai kyau na dawowar kudinta ba.

Ta yi barazanar yin tsirara a tsakiyar banki

Hayaniyar da ta tayar ta dauki hankalin kowa a farfajiyar bankin.

Bidiyon ya nuna ta tana barazanar dakatar da ayyukan banki a wannan ranar, ta sanya mukullin motarta a wuyanta kuma tana dakatar da duk wani ma'aikacin banki da ta gani zai kula kwastoma

A cikin faifan bidiyon da ya kai sama da mintuna 34, lallabin ma’aikatan banki da jami’an tsaro da wasu kwastomomi da suka damu bai tsinana komai ba face kara mata fushi.

A lokaci guda, ta yi barazanar tafiya tsirara kuma ta sha alwashin kwana a cikin banki a wannan dare.

Kara karanta wannan

Bidiyon jaruma Umma Shehu tare da diyarta yayin da suke girgijewa ya haifar da cece-kuce

Kalli bidiyon a kasa:

Abu Abdurrahman ya ce:

“Na yi amfani da na’urar ATM a bankin Zenith Bank na hanyar Kano da ke Sokoto a 2012, na’urar ta kirga kudin (N20,000) ba ta bani ba, na ji lokacin da kudin suka fadi a cikin injin, sai aka cire min kudi.
"Shikenan, har yau, ba a dawo min kudina ba. Zenith."

Akparawa Offiong Bassey ya ce:

"Wannan shine 'python dance' lol... wani lokacin, wannan shine yaren da mutane ke fahimta da sauri. Ci gaba da aikin madam."

Ezekiel Apaji Danjuma yace:

“Bankunan Najeriya dole ne ku rika rokonsu kamar taimakonku za su yi.
"Abin bakin ciki.
“Ya kamata bankin Zenith Plc ya lura da yadda ake wulakanta mutane a rassansu.
"Wasu daga cikin ma'aikatan na hada kai da masu aikata laifuka domin yin sata daga talakawan Najeriya."

Rabo a kan rabo: Baiwar Allah ta haifi yara biyu a lokaci daya, kuma ba tagawaye ba ne

Kara karanta wannan

Labarin Mary Ann: Hotunan Matar da ta fi kowa muni a duniya kuma ta ci gasar munana

A wani labarin, wata mata ta bada labarin yadda ta dauki ciki a lokacin da ta ke dauke da wani juna biyun. Kwanaki biyar ne tsakanin daukar cikin ‘ya ‘yan na ta. Wannan labari mai ban mamaki ya zo a jaridar Daily Mail.

Odalis Martinez ta bayyana yadda dadi ya kusa kashe ta bayan ta gano tana da ciki a karshen 2020.

A cewar Odalis Martinez, ta samu juna-biyun ne ‘yan watanni kadan bayan ta yi bari. A lokacin da ta je yin awo, sai ta gano ashe ‘ya ‘ya har biyu ma za ta haifa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel