Rabo a kan rabo: Baiwar Allah ta haifi yara biyu a lokaci daya, kuma ba tagawaye ba ne

Rabo a kan rabo: Baiwar Allah ta haifi yara biyu a lokaci daya, kuma ba tagawaye ba ne

  • Miss Odalis Martinez ta haifi yara biyu a lokaci daya amma kuma jariran na ta ba tagwaye ba ne
  • Wannan mata mai shekara 25 ta dauki ciki bayan tayi bari, sai kuma ta sake samun wani rabon
  • Da aka yi awo sai malamar asibiti ta fada mata cewa yara biyu ne a cikinta, tazararsu kwana biyar

California - Wata mata ta bada labarin yadda ta dauki ciki a lokacin da ta ke dauke da wani juna biyun. Kwanaki biyar ne tsakanin daukar cikin ‘ya ‘yan na ta.

Wannan labari mai ban mamaki ya zo a jaridar Daily Mail. Odalis Martinez ta bayyana yadda dadi ya kusa kashe ta bayan ta gano tana da ciki a karshen 2020.

A cewar Odalis Martinez, ta samu juna-biyun ne ‘yan watanni kadan bayan ta yi bari. A lokacin da ta je yin awo, sai ta gano ashe ‘ya ‘ya har biyu ma za ta haifa.

Kara karanta wannan

Yadda Aka Yi Rabon Biredi A Wajen Wani Kasaitaccen Biki Na Gani Na Fada, Bidiyon Ya Ja Hankali

Wannan mata mai shekara 25 a Duniya ta fahimci cewa ta dauki cikin kowane yaro ne lokaci dabam a cikin mako daya, tazarar kwanaki biyar ne a tsakani.

Masana sun san da zaman irin wannan juna-biyu wanda ake kira ‘superfetation’ da Ingilishi.

Odalis Martinez
Odalis Martinez da juna biyu Hoto: www.mirror.co.uk
Asali: UGC

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Lilo da Imelda Martinez-Atoyac

A cewar ta, ‘ya ‘yan na ta masu suna Lilo da Imelda Martinez-Atoyac su na yanayi da juna, har mai gidanta Odalis ya kan fadawa mutane cewa su ‘yan biyu ne.

“Na samu ciki a lokacin da nake dauke da wani ciki.”
“Na kan ce tagwaye ne, amma da nayi bincike, na gano lallai ba ‘yan biyun ba ne, amma abin yana da wahalar fahimta, saboda haka sai kurum in ce tagwayen ne.”
“Wasu lokutan ni da mijina, musammam mai gidana, ba ya gane su, suna rudar da shi.” - Odalis Martinez

Kara karanta wannan

Wasu Shugabannin PDP na Neman Tada Rikici, Sun ce An Ware Su a Yakin Zaben Atiku

An samu rabo bayan bari

NY Post ta ce Odalis da Antonio sun yi aure a shekarar 2020 kuma su na neman haihuwa, har an samu rabo sai kuma tayi bari, daga baya ciki ya sake shiga a watan.

“Da ake awo, sai matar ta fara gaba-tana baya, ina tunanin me ya faru, ina tsoron a fada mani labari mara dadi, sai ta ce mani ta gano wani jinjirin a cikinta."

Yakin Rasha v Ukraine

Ku na da labari cewa akwai wasu jaruman ‘yan wasan Duniya, shahararren mawaki da suke cikin rundunar sojojin Ukraine da ke yakar Rasha a halin yanzu.

Tsohuwar sarauniyar kyau ta Ukraine, Anastasia Lena ta dauki makami domin ta kare kasarta, haka zalika tsohon shugaban kasar na Ukraine, Petro Poroshenko.

Asali: Legit.ng

Online view pixel