Bidiyon jaruma Umma Shehu tare da diyarta yayin da suke girgijewa ya haifar da cece-kuce

Bidiyon jaruma Umma Shehu tare da diyarta yayin da suke girgijewa ya haifar da cece-kuce

  • Jama'a sun tofa albarkacin bakunansu bayan bayyanar wani bidiyo na jarumar Kannywood, Umma Shehu tare da diyarta suna rawa da waka
  • Da dama sun yi tir da bidiyon yayin da suke ganin hakan bai dace ba ga uwa wacce ita ce mai bayar da tarbiya ga yaranta
  • Hakan na zuwa ne yan kwanaki bayan jarumar ta fito ta yi martani ga masu zaginta, inda ta ce suna ji suna gani za ta shige aljannah ta barsu a madakata

Wani bidiyo na shahararriyar jarumar Kannywood, Umma Shehu, ta haifar da cece-kuce a shafukan soshiyal midiya.

A cikin bidiyon wanda mufeeda_rasheed1 ta daura a shafinta na Instagram, an gano jarumar tare da diyarta suna rawa tare da rera wata wakar soyayya.

Bidiyon jaruma Umma Shehu tare da diyarta yayin da suke girgijewa ya haifar da cece-kuce
Bidiyon jaruma Umma Shehu tare da diyarta yayin da suke girgijewa ya haifar da cece-kuce Hoto: dimokuradiyya.com.ng
Asali: UGC

Sai dai hakan bai birge wasu ba inda suka ta yin suka kan cewa wanene zai yiwa wani fada a tsakanin uwar da yar tata.

Kara karanta wannan

Kisan Kebbi: 'Yan majalisa sun roki FG ta tura sojojin sama da kasa domin ragargazar 'yan bindiga

Kamar yadda kuka sani ba wannan bane karo na farko da jama’a ke yin caaa a kan jarumar, domin tana daya daga cikin jarumai mata da ake bibiyar duk wani motsinsu domin ganin sun yi dan kuskure.

Sai dai ga dukkan alamu hakan bai taba damun jarumar ba domin duk da sukan da take yawan sha, baya hana mata yin abubuwan da ta sa gaba da sunan gudun maganar mutane.

Kalli bidiyon a kasa:

Martanin mutane

Legit Hausa ta tattaro wasu daga cikin martanin da mutane suna yi kan bidiyon a kasa:

ummytah__noor ta yi martani:

"Waye zayyiwa wani fada anan ‍♀️‍♀️‍♀️babu babbar asara awurin namiji yakasa nutsuwa ya samarwa yaranshi uwa tagari"

majeed_taheer ya ce:

"Allah ya wadaran naka ya lalace"

abbatyn_kawo ya ce:

Kara karanta wannan

Labarin Mary Ann: Hotunan Matar da ta fi kowa muni a duniya kuma ta ci gasar munana

"Ya Allah ubangiji ka kawo mana karshen wannan balai Amin Thumma Amin"

adoalhassanaf ya ce:

"Tarbiya iya Tarbiya"

meena_classycaps ta ce:

"@mufeeda_rasheed1 chab, ai mamana ko sunana ma bata Iya fada talk less of ya tsaya rana rawa Dani har tana wani kashe ido‍♀️ saboda kunya irinta hausa fulani. Allah ka shirya mana zuri’a"

Mutane su gama aibatani a zo ranar lahira su ga na shige Aljanna na barsu - Umma Shehu

A baya mun ji cewa, Umma Shehu ta yi tsokaci a kan aibata ta da wasu mutane ke yi, sakamakon kallo da suke yi mata a matsayin mai aikata sabon Ubangiji.

A wani bidiyo da sashin Hausa na BBC ya fitar, an jiyo jarumar tana fadin cewa ita da zunubinta ta damu ba da na wani ba sannan kuma cewa duk a laifukan da take aikatawa bata hada Allah da wani.

Jarumar ta kuma bayyana cewa tana cika salollinta guda biyar, don haka Allah mai gafara ne, idan ta roke sa cikin kuka zai yafe mata.

Kara karanta wannan

Aure ya yi albarka: Hotunan magidancin da ya auri mata 2 a rana guda yayin da suke murnar cika shekara 1

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng

Online view pixel