Kisan Kebbi: 'Yan majalisa sun roki FG ta tura sojojin sama da kasa domin ragargazar 'yan bindiga

Kisan Kebbi: 'Yan majalisa sun roki FG ta tura sojojin sama da kasa domin ragargazar 'yan bindiga

  • Yan majalisar wakilai daga jihar Kebbi sun koka a kan hare-haren da yan bindiga ke kaiwa garuruwan jihar
  • Sun bayyana cewa maharan na kashe mutane da kwashe dukiyoyinsu sannan su yi garkuwa da wasu ba tare da tangarda ba
  • Majalisar ta bukaci gwamnatin tarayya da ta tura sojojin sama da kasa da sauran jami'an tsaro domin su kai yaki har sansanin miyagun

Abuja - The Cable ta rahoto cewa yan majalisar wakilai daga Kebbi sun koka kan cewa yan bindiga na cin karensu babu babbaka a jihar.

Yan majalisar sun magantu ne a yayin zaman majalisa a ranar Laraba, 9 ga watan Maris, yayin da suke daukar nauyin wani kudiri da ke bukatar kulawar gaggawa.

Sun yi wa kudirin take da: “Bukatar kira ga gwamnatin tarayya da ta dakatar da hare-haren yan fashi da ke gudana a yankin Kebbi ta kudu.”

Kara karanta wannan

Yan bindiga sun kashe manoma 2 sannan sun yi garkuwa da wasu mutane 4 a Sokoto

Kisan Kebbi: 'Yan majalisa sun roki FG ta tura sojojin sama da kasa domin ragargazar 'yan bindiga
Kisan Kebbi: 'Yan majalisa sun roki FG ta tura sojojin sama da kasa domin ragargazar 'yan bindiga Hoto: Premium Times
Asali: UGC

Da yake jagorantar muhawara kan kudirin, Tanko Sununu, wanda ya jagoranci daukar nauyin kiran, ya ce kashe-kashe da garkuwa da mutane ya mayar da yara da yawa marayu.

Legit Hausa ta kawo a baya cewa yan bindiga sun kashe yan sa kai sama da guda 60 bayan sun farmaki garuruwa a jihar Kebbi.

Yan majalisar na Kebbi sun fayyace halin da ake ciki

Da yake magana a madadin takwarorinsa, Sununu ya ce:

“A baya an bayyana jihar Kebbi a matsayin daya daga cikin jihohi masu zaman lafiya a Najeriya har sai a shekaru kadan da suka gabata.
“Rashin tsaro a yankin Kebbi ta kudu ya janyo wahalhalu da asarar rayuka da dukiyoyi masu daraja, lamarin da ya jawo matsalar jin kai sakamakon fashewar wani abu da ya faru a cikin ‘yan gudun hijira daga garuruwa da dama.

Kara karanta wannan

Wahalar Mai: Annaru ta ci dan bunburutu da matarsa da sukayi ajiyan jarkokin mai a gida

“Kimanin kwanaki 10 da suka wuce, yan bindiga daga jihohin da ke makwabta sun farmaki yankin, inda suka kashe mutane da dama ciki harda yara da mata, sannan suka sace mutane da yawa, suka yi fashin shanu sannan suka koma sansaninsu ba tare da kalubale ba.
“A watanni shida da suka gabata, irin haka ya yi sanadiyar garkuwa da mutane da dama, ciki har da daliban kwalejin gwamnatin tarayya, wadanda har yanzu wasun su na tsare.
“A kwanaki uku da suka shige-har yanzu yana guda, yan bindiga sun farmaki yankin ba tare da kalubale ba, wannan harin ya kai ga kisan yan sa kai sama da 60.
“Wannan hare-hare na baya-bayan nan ya mayar da mata zawarawa, yara da dama sun zama marayu sannan iyalai da dama sun shiga zullumi. Ya kuma gurguntar da ayyukan tattalin arziki. Makarantu da dama dalibai da malamai sun barsu duk da cewar ana zangon karatu a yanzu."

Kara karanta wannan

Mazauna sun tsere daga kauyukan Filato yayin da yan bindiga ke tsananta kai hare-hare

Majalisa ta nemi FG ta tura sojoji ta sama da kasa zuwa yankunan

Bayan sauraron kudirin, majalisar ta bukaci gwamnatin tarayya da ta tura sojoji na kasa da sama, da sauran jami’an tsaro domin su kai yaki har zuwa sansanin yan bindigar sannan su kawo karshen kashe-kashen cikin dan kankanin lokaci, Premium Times ta rahoto.

Yan majalisar sun kuma bukaci a sanya dokar ta baci a kan tsaro a yankin arewa maso yamma da dukka sauran yankunan kasar da abun ya shafa.

Bayan Kashe Ƴan Sakai 57, Ƴan Bindiga Sun Sake Kashe Sojoji 13, Ƴan Sanda 5 Da Vigilante a Kebbi

A wani labarin kuma, mun ji cewa yan bindiga sun sake kashe jami'an tsaro 19 cikinsu akwai sojoji 13, a jihar Kebbi, a cewar wata majiyar tsaro da mazauna gari a ranar Laraba, rahoton The Punch.

An yi artabun ne a daren ranar Talata a kauyen Kanya da ke Danko-Wasagu, kwana guda bayan an kashe dimbin yan sakai a yankin.

Kara karanta wannan

Zamfara: Yan bindiga sun bude wa juna wuta a kasuwa, rayuka da dama sun salwanta

Daruruwan yan bindiga sun afka Kanya, inda suka fafata da sojoji da yan sanda na tsawon awa uku a cewar majiya da kuma mazauna garin.

Asali: Legit.ng

Online view pixel