Ta leko ta koma: Attajiri ya goge fuskar ango da amarya da kudi, amma ya kwashi abin sa ya tafi

Ta leko ta koma: Attajiri ya goge fuskar ango da amarya da kudi, amma ya kwashi abin sa ya tafi

  • Wani mai amfani da shafin soshiyal midiya ya koka bayan wallafa bidiyo na wani attajiri da ya lika daloli a wajen wani aure da aka yi a jihar Imo
  • A cikin bidiyon dai, an gano attajirin yayin da ya goge fuskar ango da amarya da kudi, amma bayan nan sai ya kwashi abin sa ya tafi
  • Jama’a sun tofa albarkacin bakinsu kan haka, yayin da wasu ke hango illar da ke tattare da abun da mutumin ya yiwa sabbin ma’auratan

Imo - Jama’a sun tofa albarkacin bakunansu bayan abun al’ajabi da wani mutum ya aikata a wajen wani taron aure da aka yi a jihar Imo.

A wani bidiyo da shafin @lindaikejiblog ya wallafa a Instagram, an gano lokacin da wani attajiri ya goge fuskokin amarya da ango da kudi sannan kuma ya kwashe kudin ya tafi da su.

Kara karanta wannan

Yan sanda sun bayyana gaskiyar abin da yasa Fulani Makiyaya suka halaka mutum 7 a Taraba

Ta leko ta koma: Attahiri ya goge fuskar ango da amarya da kudi, amma ya kwashi abin sa ya tafi
Ta leko ta koma: Attahiri ya goge fuskar ango da amarya da kudi, amma ya kwashi abin sa ya tafi Hoto: Facebook/Munachi Harry, Maxwell Monty
Asali: Getty Images

A cewar wani mai amfani da Facebook Munachi Harry wanda shine ya bayyana labarin abun da ya faru, ya ce mutumin ya aikata hakan ne bayan ya yiwa ma’auratan ruwan daloli.

Da yake kokawa kan lamarin, Munachi ya dasa ayar tambaya kan dalilin da yasa ya share fuskokin ma’auratan da kudin sannan kuma cewa menene dalilin mutumin na tafiya da kudin maimakon ya barsu a kasa kamar yadda kowa ke yi.

Mutumin ya yiwa ma’auratan addu’an tsallake wannan tuggu sannan ya bukaci mutane da su dunga yin taka-tsan-tsan.

A cikin bidiyon, an jiyo mutane suna ta jinjinawa mutumin yayin da yake barin wajen.

Kalli bidiyon a kasa:

Jama’a sun yi martani a kan lamarin

etimajonathan ta yi martani:

"Na tabbata babu wanda ya lura har sai da suka kalli bidiyon (watakila kwanaki bayan hakan)"

Kara karanta wannan

Kisan gilla kan Musulmai: Wani ya tashi bam a masallacin Juma'ah, mutum 56 sun rasu

kellyjada.nez ta ce:

"Ma'auratan da suka tsaya kamar gumaka sun fi damuna."

briscoins ya ce:

"Allah ya sani zan rike hannunsa sannan na karbi dalolin"

miscreantcomedy ya ce:

"Me yasa basu rike shi ba, sannan su tambaye shi kafin ya tafi?"

Yin aure kuskure ne da na tafka a rayuwata kuma ba zan kara ba, Magidanci na neman sakin matarsa

A wani labari na daban, wani mutum dan Afirika ta kudu, Miles Montego, ya azabtu bayan aurensa ya ki dadi.

Mutumin da ya taba auren ya jawo cecekuce a kafafan sada zumuntar zamani na Twitter, bayan ya wallafa abunda ya siffanta da babban kuskuren da ya taba aikatawa.

Miles Montego ya ce, auren da yayi shi ne babban kuskuren da ya taba tafkawa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel