Kisan gilla kan Musulmai: Wani ya tashi bam a masallacin Juma'ah, mutum 56 sun rasu

Kisan gilla kan Musulmai: Wani ya tashi bam a masallacin Juma'ah, mutum 56 sun rasu

  • Wasu 'yan bindiga sun kai hari masallaci ana tsaka da sallar Juma'a, inda suka ta da bam a cikin masallacin
  • Rahotanni sun bayyana cewa, mutane sama da 50 ne suka rasu tare da samun wadanda suka samu munanan raunuka
  • Wannan lamari dai ya faru ne Peshawar, har yanzu ba a gano wadanda suka aikata mummunan aikin ba

Peshawar, Pakistan - Wani rahoton Reuters ya bayyana cewa, wani bam mai karfi ya tashi a cikin wani masallacin 'yan Shi'a da ke birnin Peshawar a Arewa maso Yammacin Pakistan, inda ya kashe mutane fiye da 50 tare da jikkata wasu da dama.

Fashewar bam din ta faru ne a lokacin da mutane suka taru a masallacin Kucha Risaldar da ke yankin tsohon birnin na Peshawar domin yin sallar Juma'a.

Kara karanta wannan

Jakadan Canada a Najeriya ya ziyarci marasa gata a kasan gada, hotunansu suna wasa sun taba zukata

An dasa bam a masallaci a Pakistan
Kisan gilla kan Musulmai: Wani ya tashi bam a masallacin Juma'ah, mutum 56 sun rasu | Hoto: aljazeera.com
Asali: UGC

Jami’an asibitin sun ce akalla mutane 56 ne suka rasu yayin da akalla mutane 194 aka ruwaito sun jikkata, inji rahoton AlJazeera.

Har yanzu dai babu wata kungiya ko wasu mutane da suka amsa kai wannan mummunan hari.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Shugaban ‘yan sandan Peshawar Muhammed Ejaz Khan ya ce rikicin ya faro ne lokacin da wasu mahara biyu dauke da makamai suka bude wuta kan ‘yan sanda a wajen masallacin.

An kashe maharin daya da dan sanda daya a arangamar, sannan wani dan sanda ya samu rauni. Sai daya maharin ya shiga cikin masallacin ya tayar da bam.

Yadda lamarin ya faru

Wani shaida da ya bayyana sunansa da Naeem da ke da zama a kusa da masallacin ya shaida cewa:

"Da farko na ji karar harbe-harbe biyar zuwa shida, sannan na ga dan kunar bakin wake ya shiga cikin masallacin sai wata babbar fashewa ta faru.

Kara karanta wannan

An tsinci gawar saurayi da Budurwa a cikin Mota, ana zargin suna saduwa suka mutu

“Kofofin gidana sun bude da duka, na fadi kasa. Lokacin da na shiga masallacin sai ga hayaki da kura ga kuma mutane suna kwance cikin jini”.

Sashen kwance bama-bamai ya ce an yi amfani da bam mai nauyi kimanin kilogiram 5 wajen aikata barnar.

Motocin daukar marasa lafiya sun bi ta kan tarkatattun titunan da ke gefe tare da kai wadanda suka jikkata zuwa asibitin Lady Reading.

Firayim Minista Imran Khan yayi Allah wadai da tashin bam din.

'Yan bindiga sun sake kai hari masallaci a Neja, sun kashe 15 sun raunata da dama

A wani labarin, a kalla masallata 15 ne suka mutu yayin da wasu da dama suka samu rauni a harin da aka kai a masallaci da ke kauyen Ba'are a karamar hukumar Mashegu na jihar Neja.

Maharan sun kai harin ne yayin da mutanen kauyen ke sallar asubahi kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Babu dadi: IGP ya koka kan yadda 'yan sanda ke amfani da makamai ta wasu hanyoyi

Wata majiya ta ce an garzaya da wadanda suka jikkata zuwa babban asibitin Kontagora domin yi musu magani.

Asali: Legit.ng

Online view pixel