Da Dumi-Dumi: Matar Abdulmalik Tanko ta ba da shaida a Kotu kan kisan Hanifa Abubakar

Da Dumi-Dumi: Matar Abdulmalik Tanko ta ba da shaida a Kotu kan kisan Hanifa Abubakar

  • Matar wanda ake zargi da kashe Hanifa Abubakar, Jamila Muhammad, ta ba da shaida a Kotu bayan ya ce ba shi ya kashe ta ba
  • Jamila ta faɗi yadda ya kawo mata yarinyar da kuma karyar da ya mata game da ita, har zuwa ranar da ya ɗauke ta da daddare bayan kwana 5
  • Lauyan gwamnati kuma Antoni Janar na jahar Kano ya gabatar da shaidu takwas kenan zuwa yanzu

Kano - Jamila Muhammad Sani, matar sunnah ga Abdulmalik Tanko, wanda ya faɗi yadda ya kashe Hanifa Abubakar a farko, ta ba da shaida a kansa ranar Alhamis.

Daily Trust ta rahoto cewa Babbar Kotun dake zamanta a Audu Bako karkashin jagorancin mai Shari'a Usman Na'abba ta cigaba da sauraron shari'ar.

Kara karanta wannan

Rashin tsaro: Dan takarar shugaban kasa ya je neman shawari wurin Sheikh Gumi

Shaidun masu gabatar da ƙara bisa jagorancin Antoni Janar na jihar Kano kuma Kwamishinan shari'a, Musa Lawan.

Mutum uku da ake zargi
Da Dumi-Dumi: Matar Abdulmalik Tanko ta ba da shaida a Kotu kan kisan Hanifa Abubakar Hoto: dailynigerian.com
Asali: UGC

Lauyan gwamnatin Kano ya gabatar da shaidu uku a ranar 2 ga watan Maris, 2022, wanda suka haɗa da jami'an DSS biyu da Insufektan yan sanda.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Da yake kara gabatar da shaidu kamar yadda ya alƙawarta, Lauyan ya kira wata mata da kuma Jamila a matsayin shaidu na hudu da na biyar.

Yayin da ta tsaya a gabatan Kotu, Jamila ta bayyana kanta a matsayin matar da suka yi auren sunnah da Tanko, kuma mutum na biyu, Hashim, abokinsa ne tun lokacin da ta san su.

A jawabinta tace:

"Ya kawo yarinyar gidana kuma ya faɗa mun mahaifiyarta malama ce a makarantarsa, ta samu aiki a Saudiyya kuma zata je Abuja ta sanya hannu a wasu takardu."

Kara karanta wannan

Kano: Shaidu sun gabatar da abubuwa 10 da suka gano game da kisan Hanifa Abubakar

"Gari ya waye, yamma ta yi amma shiru, na tambaye shi ina mahaifiyar yarinyar nan take? Sai ya faɗa mun bata kira shi ba amma da ya kirata tace layi ya rike ta, ba zata dawo ranar ba."
"Ta kara kwana biyu, sai ce mun ya yi ta kira shi wai kuɗi sun kare mata a Kaduna. Daga nan na daina tambayarsa saboda ya ce ba ta da kuɗin dawowa. Ranar da ya kawo ta gida ta fara kuka, sai ya haɗa ta da 'ya'yanshi Safiya da Aisha."

Shin yarinyar ita ce Hanifa?

Jamila ta tabbatar da cewa yarinyar da maigidanta ya kawo mata ita ce a hoton da aka nuna mata a zaman Kotu.

Ta kara da cewa:

"Bayan kwana 5 yace zai kaita gida, lokacin da daddare ne, na ɗauki kayan makarantarta na bashi, kawayenta na bacci lokacin. Na nemi ya bari sai da safe saboda suna bacci amma ya matsa."

Kara karanta wannan

Da duminsa: Gwamnatin tarayya ta amince a mikawa Amurka Abba Kyari

"Mun yi wannan maganganun ne tsakanin karfe 7-11:00 na dare. Da karfe 11:00 na dare ya fita da ita, lokacin da ya dawo na yi bacci, dan haka ban san ainihin lokacin da ya dawo ba."
"Ta kuma yi bayanin baje, kaya da Hijabin dake jikin yarinyar lokacin da ya kawo ta gida da kuma lokacin da aka kashe ta."

Lauyan waɗan da ake kara, MA Usman ya mata tambayoyi kafin Kotu ta sallame ta, yayin amsa masa ne ta faɗi cewa Mijinta ya faɗa mata sunan mahaifiyar yarinyar Murja.

"Ba mu cika shiga gidajen makota ba sai idan ana wani sha'ani, babu wanda ya kawo mun gida sai Hanifa. Ya kawo ta ranar Asabar ya ɗauke ta ranar Alhamis. Babban ɗan mu shekarunsa 4."

Zuwa yanzun masu kara sun gabatar da shaidu Takwas kenan, a halin yanzun an ɗage zama zuwa 9 da 10 ga watan Maris.

A wani labarin kuma Wani bawan Allah ya daba wa dan Acaba makami har lahira kan ya buge masa Kare a Gombe

Kara karanta wannan

Babu dadi: IGP ya koka kan yadda 'yan sanda ke amfani da makamai ta wasu hanyoyi

Jami'an yan sanda sun cafke wani matashi, Ibrahim Sa'idu, da ya halaka ɗan Acaba da makami kan ya yi kuskuren kade masa kare a Gombe.

Kwamamishinan yan sandan jihar, Ishola Babaita, ya ce Karen da aka buge bai mutu ba, kuma mai laifin ya amsa tuhumar da ake masa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel