Masarautar Katsina: Jerin yan takara 3 da ke neman kujerar Wazirin Katsina

Masarautar Katsina: Jerin yan takara 3 da ke neman kujerar Wazirin Katsina

  • Bayan murabus din Wazirin Katsina, Farfesa Sani Abubakar Lugga, masarautar Katsina na shirin cike gurbin da wani
  • Zuwa yanzu dai an samu manyan yan takara uku da suka nuna sha'awarsu ta son darewa kujerar da Lugga ya bari daga gidajen Waziri biyu
  • Wadannan yan takara sune Sarkin Fadan Katsina, Abdulkadir Ismaila, Abdulaziz Isa Kaita da kuma Waziri Hamza Zayyad

Katsina - An fara hada-hadar shirya zaben maye gurni a Katsina yayin da manyan yan takara uku suka nuna ra’ayinsu na son darewa kujerar Wazirin Katsina bayan murabus da tsohon Waziri, Farfesa Sani Abubakar Lugga ya yi.

Yan takara biyu sun fito ne daga gidan Waziri Haruna kuna sune Sarkin Fadan Katsina, Abdulkadir Ismaila, dan majalisar masarautar Katsinan da kuma Abdulaziz Isa Kaita, dan Waziri Isa Kaita.

Kara karanta wannan

2023: Sarkin Katsina Ya Goyi Bayan Tinubu Ya Gaji Kujerar Buhari

Dan takara na uku, Maliki Zayyad, kani ga marigayi Waziri Hamza Zayyad, ya kuma fito ne daga gidan Waziri Zayyana, Daily Trust ta rahoto.

Masarautar Katsina: Jerin yan takara 3 da ke neman kujerar Wazirin Katsina
Manyan yan takara 3 ne ke neman kujerar Wazirin Katsina Hoto: punchng.com
Asali: UGC

Masarautar Katsina tana da daular sarakuna biyu da gidan Waziri biyu. Na farko sune daular Dallazawa karkashin Sarki Ummarun Dallaje wanda ya fito daga masu rike da tutar Khalifancin Sakkwato. Ya hau karagar mulki a shekarar 1806/07.

Na biyun shine daular Sullubawa daga Turawan Ingila wanda ya nada Sarkin Katsina Muhammadu Dikko a shekarar 1906/07.

An nada Waziri Haruna a shekarar 1906/07 a matsayin Wazirin Katsina na farko tare da amincewar Birtaniya daga Sarki Muhammadu Dikko. An nada Waziri Zayyana ne a shekarar 1928 bayan sake fasalin mulki a arewacin Najeriya.

Domin karfafa alaka, Sarki Dikko ya aurawa dansa diyar Waziri Haruna wanda daga bisani ya zama Sarki Usman Nagogo daga daular Sullubawa.

Kara karanta wannan

Da Ɗuminsa: Buhari Ya Naɗa Magajin Farfesa Sulaiman Bogoro A TETFund

Ita ce mahaifiyar marigaji Janar Hassan Usman Katsina.

Bugu da kari, Sarki Usman Nagogo ya aurawa dansa diyar Waziri Zayyana wanda ya yi nasarar zama Sarki Muhammadu Kabir Usman.

Ita ce mahaifiyar Durbin Katsina, Aminu Kabir.

Rahoton ya nuna cewa dukka gidajen Waziri biyun suna da alakar auratayya da daular Dikko, wanda daga nan ne sarki mai ci, Dr Abdulmumini Kabir Usman ya fito.

Wazirin Katsina ya yi murabus daga kan kujerarsa bayan wata takaddama da ta biyo jawabinsa a Ilorin

A baya mun ji cewa Farfesa Sani Abubakar Lugga, Wazirin Katsina, ya yi murabus daga majalisar masarautar jihar.

Hakan ya biyo bayan tuhumar da majalisar ta yi masa kan cewa ya tattauna batutuwan rashin tsaro a Ilorin, jihar Kwara, ba tare da yardar masarautar ba.

A ranar 14 ga watan Fabrairu ne Farfesa Lugga ya halarci wani taro a Ilorin inda ya bayyana cewa yawan hare-haren yan bindiga ya yi sanadiyar rufe makarantu a kananan hukumomi takwas na jihar Katsina.

Kara karanta wannan

AbdulJabbar ya gabatar da litattafai 27 a kotu, ya rantse da Al-Qur'ani bai zagi Annabi ba

Asali: Legit.ng

Online view pixel