Ana ga yaki: Bidiyon auren sojojin sa kai na Ukraine a fagen daga tsakanin Rasha da Ukraine

Ana ga yaki: Bidiyon auren sojojin sa kai na Ukraine a fagen daga tsakanin Rasha da Ukraine

  • Wasu mambobi biyu na rundunar tsaron sa kai ta Ukraine sun yi aure a wani kwaryakwaryan biki duk kuwa da mamayar da sojojin Rasha suka yi a kasar
  • Lesia Ivashchenko da Valerii Fylymonov sun yi musayar alkawarin daurin aure a ranar Lahadi, 6 ga watan Maris, a wani shingen bincike a Kyiv.
  • Ma'auratan suna kewaye da wasu gungun abokan aikinsu sojoji, inda suke rera waka wasu kuwa na kada ana cashewar murnar biki

Kyiv, Ukraine - A yayin da Rasha ta mamaye kasar Ukraine, wasu mambobi biyu na rundunar tsaron sa kai na kasar Ukraine sun yanke shawarar daukar matakin rayuwarsu zuwa gaba.

Wani rahoto da kafar yada labarai ta ABC ta fitar ya nuna cewa Lesia Ivashchenko da Valerii Fylymonov da ke cikin rundunar tsaron kasar Ukraine sun yi musayar alkawarin aure a wani shingen bincike a birnin Kyiv.

Sojoji ma'aurata 'yan Ukraine
Ana ga yaki: Bidiyon auren wasu sojojin sa kai na Ukraine a fagen daga tsakanin Rasha da Ukraine | Hoto: @KyivPost
Asali: Twitter

Sojojin na sa kai sun yi aure ne a fagen daga sanye da kakin soja a ranar Lahadi, 6 ga Maris. Amarya, Lesia sanye da hular kwano ta soja akan farin mayafinta na aure an hangeta dauke da fulawar aure.

Lokacin da ita da ango suka tabbatar da bikin aurensu ta hanyar sumbatar juna, sai amarya ta sauya hular kwano da mayafin aure, in ji rahoton Daily Mail.

Paul Ronzheimer, dan jaridar kasar Jamus ne ya yada bidiyon bikin auren inda wasu gungun sojoji suke taya ma'auratan murna.

Wani sako a shafin Twitter da KyivPost ya yada, ya tabbatar da cewa limamin soja ne ya daura auren mayakan biyu a fagen yakin Ukraine da Rasha.

Zakaran damben boksin na duniya na Tormer wanda daga baya ya tsunduma siyasa, magajin garin Kyiv Vitali Klitschko, ya ce ya samu damar gaisawa da ango da amaryar.

Sai kun biya N560k: Ukraine ga 'yan Najeriyan da ke son taya ta yakar Rasha

A wani labarin, ofishin jakadancin Ukraine a Najeriya ya ce 'yan Najeriya da ke son zuwa Ukraine don yakar sojojin Rasha dole ne su amince da biyan dala 1,000 (kwatankwacin N560,000) kowannen saboda a samar musu da tikiti da biza.

Ofishin Jakadancin ya bayyana haka ne a lokacin da ‘yan sa kai daga Najeriya suka yi dandazo a harabarta a Abuja ranar Alhamis domin bayyana shirinsu na shiga Ukraine da Rasha, inji rahoton Leadership.

Sakatare na biyu a ofishin jakadancin Ukraine a Najeriya, Bohdan Soltys, ya tabbatar da cewa kowane dan Najeriyan da ke son zuwa Ukraine zai biya dala 1,000.

Asali: Legit.ng

Online view pixel