Da Duminsa: An Sanar Da Ranar Da Rasha Da Ukraine Za Su Yi Zaman Tattauna Tsagaita Wuta

Da Duminsa: An Sanar Da Ranar Da Rasha Da Ukraine Za Su Yi Zaman Tattauna Tsagaita Wuta

Ukraine da Rasha za su yi tattaunawar tsagaita wuta domin farar hula su samu damar ficewa a ranar Litinin, a cewar wani jami'in Ukraine, bayan an dakatar da kwashe mutane daga birnin Mariupol da ke kudu maso gabashin kasar.

Ofishin shugaban kasar Ukraine, a ranar Asabar ta ce Rasha ta cigaba da yin luguden wuta a yankin, duk da tsagaita wuta da aka cimma, rahoton Vanguard.

Da Duminsa: Rasha Da Ukraine Za Su Yi Zaman Tattauna Tsagaita Wuta Ranar Litinin
Rasha Da Ukraine Za Su Yi Zaman Tattauna Tsagaita Wuta Ranar Litinin. Hoto: Vanguard
Asali: Twitter

Dakatar da kwashe mutane daga birnin na zuwa ne awa biyu bayan tsagaita wutan bayan Shugaba Volodymyr Zelenskyy ya yi wani jawabi a bidiyo ga dabban masu zanga-zanga a daren Juma'a a manyan biranen Turai.

Amma mafi yawancin sojojin Rasha suna nan ba su fasa yunkurinsu na shiga babban birnin kasar ta Kyiv ba.

Kara karanta wannan

Gwanda in zama dan gudun Hijra da in dawo Najeriya, Dan Najeriya dake Ukraine

A cewar Yahoo News, Davyd Arakhamia, shugaban jam'iyyar su Zelenskyy kuma mamba na tawagar Ukraine na tattaunawa tsakanin kasashe ya ce ranar Litinin ne za a yi tattaunawa na uku.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Zelenskyy, a ranar Juma'a ya bukaci masu zanga-zangan su goyi bayan Ukraine kan kutsen da sojojin Rasha ke musu yana mai gargadin cewa, 'Idan muka fadi, kuma kun fadi.'

A ranar Asabar, shugaban na Ukraine ya yi jawabi na neman taimako ga yan majalisan Amurka kusan 300 na tsawon awa daya ta amfani da fasahar zoom.

A bangarensa, Sakataren Amurka, Antony Blinken ya yi gargadin cewa akwai yiwuwar rikicin zai kazanta kafin sauki ya zo.

Kuma Shugaban Rasha Vladimir Putin ya yi gargadin cewa idan kasashen Yamma suka saka takunkumin hana jirage keta hazon Ukraine kamar yadda Zelenskyy ke nema, zai dauki hakan a matsayin mataki na yaki.

Kara karanta wannan

Wahalar Mai: Anyi rabon jarkokin man fetur a wani bikin hadimar gwamna a jihar Legas

Dakaci karin bayani ...

Asali: Legit.ng

Online view pixel