Sai kun biya N560k: Ukraine ga 'yan Najeriyan da ke son taya ta yakar Rasha

Sai kun biya N560k: Ukraine ga 'yan Najeriyan da ke son taya ta yakar Rasha

  • Ofishin jakadancin Ukraine a Najeriya ya bayyana irin matakan da za a bi kafin 'yan Najeriya su shiga Ukraine
  • 'Yan Najeriya da dama sun nuna sha'awar tafiya Ukraine domin taya kasar yaki da kasar Rasha da ke kai mata hari
  • Kasar Ukraine ta ce dole sai 'yan Najeriya sun biya kudin tikiti da biza kafin su iya shiga kasar ta Ukraine

FCT, Abuja - Ofishin jakadancin Ukraine a Najeriya ya ce 'yan Najeriya da ke son zuwa Ukraine don yakar sojojin Rasha dole ne su amince da biyan dala 1,000 (kwatankwacin N560,000) kowannen saboda a samar musu da tikiti da biza.

Ofishin Jakadancin ya bayyana haka ne a lokacin da ‘yan sa kai daga Najeriya suka yi dandazo a harabarta a Abuja ranar Alhamis domin bayyana shirinsu na shiga Ukraine da Rasha, inji rahoton Leadership.

Kara karanta wannan

N56,000 za mu baku: FG za ta raba wa wadanda suka dawo daga Ukraine kudin kashewa

Dole 'yan Najeriya su biya kudin yaki da Rasha
Sai kun biya N56k: Ukraine ga 'yan Najeriyan da ke son taya kasar yakar Rasha | Hoto: sawahpress.com
Asali: UGC

Sakatare na biyu a ofishin jakadancin Ukraine a Najeriya, Bohdan Soltys, ya tabbatar da cewa kowane dan Najeriyan da ke son zuwa Ukraine zai biya dala 1,000.

Soltys ya kuma shaida cewa, zai yi wahala ga 'yan sa kai su tafi zuwa Ukraine yanzu tunda an rufe sararin samaniyar kasar saboda yakin da take yi da Rasha.

Ya ce tunda ‘yan Najeriya na bukatar biza don shiga Romania da Poland, zai yi wuya su yi amfani da iyakokin kasa na kasa.

Sai dai ya kara da cewa Ukraine ba ta daukar sojojin haya daga kasashen waje, kawai tana neman 'yan sa kai da za su taya ta yakar Rasha ne, kamar yadda Punch ta ruwaito.

Don haka ya shawarci ‘yan Najeriya da kada su mayar da hankali kan kudin da za su samu, inda ya yi alkawarin cewa za a rika biyan ‘yan sa kai daga Najeriya albashi daidai da na sojojin Ukraine.

Kara karanta wannan

Da dumi-dumi: Rukunin farko na yan Najeriya mazauna Ukraine sun iso Abuja

N56,000 za mu baku: FG za ta raba wa wadanda suka dawo daga Ukraine kudin kashewa

A wani labarin, shugabar hukumar ‘yan Najeriya mazauna kasashen waje (NIDCOM), Abike Dabiri-Erewa, ta ce karin jirage guda biyu da ke kwashe ‘yan Najeriya daga kasar Ukraine za su iso a yau dinnan.

Kashi na farko na 'yan Najeriya da suka tsere daga mamayar da Rasha ta yi wa Ukraine sun iso Abuja da safiyar yau Juma'a.

‘Yan Najeriya 411 da suka hada da dalibai da ma’aikatan ofishin jakadanci sun isa filin jirgin saman kasa da kasa na Nnamdi Azikwe da ke Abuja da safiyar yau.

Asali: Legit.ng

Online view pixel