Matasa sun fusata, sun damke yan bindiga biyu sun kona su kurmus

Matasa sun fusata, sun damke yan bindiga biyu sun kona su kurmus

  • Wasu da ake zargin masu garkuwa da mutane ne sun rasa rayukansu a hannun matasan kauyen Anpam dake jihar Filato
  • Fusatattun matasan sun halaka su, tare da kona gawarwakinsu saboda fushin hana su zaman lafiya da kwanciyar hankali
  • Hukumar yan sanda ta jihar ta tabbatar da aukuwar lamarin, ta ce kwamishinan yan sanda ya ɗauki mataki tun da farko

Plateau - Wasu da ake zargin yan bindiga ne masu garkuwa da mutane sun rasa rayukansu a hannun mutane, kuma suka kona gawarsu ƙurmus a kauyen Anpam, karamar hukumar Mangu, jigar Filato.

Daily Trust ta rahoto cewa wasu fusatattun matasa ne suka halaka mutanen da ake zargin masu garkuwa da mutane ne a yankin.

Jihar Filato
Matasa sun fusata, sun damke yan bindiga biyu sun kona su kurmus Hoto: punchng.com
Asali: UGC

Rahoto ya nuna cewa kusan gidaje 13 mallakin Fulani fusatattun matasan suka ƙone a yankim bayan ƙashe mutanen biyu.

Kara karanta wannan

Masu garkuwa da mutane sun sace mata da miji, sun hada da jariri mai wata 5

Sai dai lamarin kone gidajen da matasa suka yi ya jefa mazauna yankim cikin tashin hankali da zaman ɗar-ɗar.

Wane mataki hukumomi ke ɗauka?

Kakakin rundunar yan sanda reshen jihar, ASP Ubah Gabriel, ya tabbatar da kashe masu garkuwa da ake zargi.

Ya ce:

"Tabbas lamarin ya faru, kuma an halaka waɗan da ake zargin masu garkuwa ne. Kuma aka kone wasu gidaje. Mun samu labarin abin da ya faru a Mangu."
"Tuni kwamishinan yan sanda ya tura dakaru domin dawo da zaman lafiya da bin doka da oda a yankin baki ɗaya."
"Kuma yanzu haka akwai taron masu ruwa da tsaki dake gudana a karamar hukumar Mangu domin gano musabbabin kone gidaje da kuma tabbatar da kare mutane daga wani hari nan gaba.

Kakakin yan sanda ya ƙara da cewa taron zai lalubo hanyar magance kai wa mutane hari, da kuma yadda za'a tunkari matsalolin da ka iya tasowa.

Kara karanta wannan

Yan bindiga sun bindige tsohuwar shugabar matan PDP, diyarta da wasu mutum biyu

A wani labarin na daban kuma Dalibin da ake zargi da halaka budurwarsa ya koma mawaƙi a Kotu

Wani dalibin jami'ar Jos da ake shari'a kan zargin ya halaka budurwarsa domin yin asiri ya koma mawaki a zaman Kotu.

Ana zargin dalibin Moses Okoh da kashe budurwarsa, Jennifer, a ranar 31 ga watan Disamba na shekarar da ta gabata.

Asali: Legit.ng

Online view pixel