Wata Sabuwa: Dalibin da ake zargi da halaka budurwarsa ya koma mawaƙi a Kotu

Wata Sabuwa: Dalibin da ake zargi da halaka budurwarsa ya koma mawaƙi a Kotu

  • Wani dalibin jami'ar Jos da ake shari'a kan zargin ya halaka budurwarsa domin yin asiri ya koma mawaki a zaman Kotu
  • Ana zargin dalibin Moses Okoh da kashe budurwarsa, Jennifer, a ranar 31 ga watan Disamba na shekarar da ta gabata
  • A zaman ranar Jumu'a, masu gabatar da kara sun gabatar da shaidu biyu duk ma'aikatan Otal ɗin da aka tsinci gawar

Jos, Plateau - Dalibin jami'ai UNUJOS, Moses Okoh, dake fuskantar shari'a a babbar Kotun Jos bisa zargin kashe budurwarsa daliba, Jennifer Anthony, ya koma mawaƙi.

The Nation ta rahoto cewa Saurayin ya koma tamkar mawaƙi a zaman Kotu na ranar Alhamis, yayin da aka fara gabatar da shaidu a kansa.

Yan sanda sun zargin Okoh da aikata kisan a ranar 31 Disamba, 2021 lokacin da ake ganin ya kashe Jennifer kuma ya cire idanunta da wasu sassan jikinta.

Kara karanta wannan

Da Dumi-Dumi: Matar makashin Hanifa Abubakar ta juya masa baya a Kotu, ta faɗi gaskiyar lamari

Zaman Kotu
Wata Sabuwa: Dalibin da ake zargi da halaka budurwarsa ya koma mawaƙi a Kotu Hoto: thenationonlineng.net
Asali: UGC

Yayin cigaba da zaman sauraron ƙarar, wani shaida, Akubo Lazarus, mai kula da kwastomomi a Otal din Domus Pacis, ya faɗa wa Kotu cewa wanda ake zargin ya zo Otal ɗin su a wannan rana.

A jawabinsa ya ce:

"Wanda ake kara ya yi rijista da sunan Moses Oche yayin da ya zo Otal ɗin mu da karfe 4:00 na yammacin ranar 31 ga watan Disamba. Ya zo shi kaɗai, bayan awanni Jennifer ta zo, ya sakko ya ɗauke ta."
"Na tashi aiki a ranar na tafi gida, na dawo washe gari, ya zo domin ya gama zai tafi, sai naje duba ɗakin. Ina zuwa na tarad da gawar mace a kasa cikin jini, na yi kokarin sanar wa don a tsare shi, amma ya riga ya bar harabar Otal."

Kara karanta wannan

Rashin tsaro: Dan takarar shugaban kasa ya je neman shawari wurin Sheikh Gumi

Wata shaidar dake aiki a ɗakin girki na Otal ɗin ta shaida wa Kotu cewa ta zuba wa wanda ake zargi faranti biyu na abinci.

Alkalin kotun, mai shari'a S.P Gang, bayan sauraron shaidun da aka gabatar, ya ɗage zaman zuwa ranar 9 ga watan Maris.

Wata ta maka mijinta a Kotu kan abin da yake mata a wurin saduwa

A wani labarin kuma Mata ta kai karar Mijinta Kotu kan yana cusa mata tissue a Al'aura idan suna saduwa

Wata mata ta maka Mijinta Uban ƴaƴanta a gaban Kotu bisa zargin yana cusa mata tarkace a al'aura yayin saduwar aure.

Matar ta shaida wa alkalin Kotun a Abuja cewa ta ɗana masa tarko ta tabbatar da abin da yake mata, amma mijin ya musanta.

Asali: Legit.ng

Online view pixel