Karatowar Ramadana: Yadda masu ciwon suga za su yi azuminsu cikin sauki

Karatowar Ramadana: Yadda masu ciwon suga za su yi azuminsu cikin sauki

  • Wani masanin ciwon suga ya magantu a kan matakin da ya kamata masu cutar da ke muradin yin azumi za su dauka yayin da Ramadana ke kara karatowa
  • Dr. Oluwarotimi Olopade ya bukaci masu ciwon sukari na 2 da su zauna su yi tsare-tsare da likitocinsu kafin lokaci don sanin matakin dauka
  • Ya ce akwai bukatar a daidaita magungunansu domin kada rashin yin hakan ya kara tabarbarar da lafiyarsu

Wani kwararren likita mai suna Dr. Oluwarotimi Olopade, ya bukaci masu ciwon sukari na 2 da ke fatan yin azumi da su tattauna da likitocinsu kafin su fara.

Wannan kira na Dr Olopade na zuwa ne a daidai lokacin da watan Ramadana ke kara karatowa, wanda a cikinsa Musulmi ke yin azumi na kwanaki 29-30.

Kara karanta wannan

Da Duminsa: An Sanar Da Ranar Da Rasha Da Ukraine Za Su Yi Zaman Tattauna Tsagaita Wuta

Karatowar Ramadana: Yadda masu ciwon suga za su yi azuminsu cikin sauki
Karatowar Ramadana: Yadda masu ciwon suga za su yi azuminsu cikin sauki Hoto: The Guardian
Asali: UGC

Likitan wanda ya kuma kasance masanin ciwon suga a asibitin koyarwa na jami’ar Lagas, ya bayyana cewa akwai bukatar masu ciwon suga su zanta da likitocinsu don sanin ko sun cancanci yin azumi bisa ga matsayin lafiyarsu.

Ya ce yana iya zama dole ga wasu masu ciwon suga su ajiye azuminsu saboda yanayin lafiyarsu, Punch ta rahoto.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ya kuma ce tattaunawa kafin lokaci zai ba likitocin damar daidaita magunguna ga majinyatan da suka cancanci yin azumi domin gujewa illar da ke tattare da su da sauran matsalolin lafiya.

A cewar masanin ciwon, azumi na da muhimmanci a addinai da dama, amma idan har ba a bi shi yadda ya kamata ba, musamman bin shawarar likitoci, yana iya haifar da gagarumin matsala ga lafiyar masu ciwon sukari na biyu.

Ya ce a bisa ga alkalman baya-bayan nan na ciwon sukari na kasa da kasa, akwai mutane miliyan 24 da ke dauke da cutar a Afrika.

Kara karanta wannan

Zanga-zanga: Mata sun tare kofar majalisa saboda kin amincewa da wani kudirin mata

Alkaluman ya kuma nuna cewa Najeriya na da mutane miliyan 1.7 da ke dauke da ciwon sikari na 1 da biyu.

Illar azumi ba tare da kulawa ba ga mutumin da ke da ciwon suga, musamman ciwon sikari na 2, shine za a samu sukarin ya yi kasa ko sama.

A cewar kungiyar Zuciya ta Amurka da kungiyar masu ciwon sikari ta Amurka, azumi na iya zama mai amfani ga masu ciwon suga a cikin dan gajeren lokaci.

Sai dai kuma, sun bayyana cewa babu wani dogon bincike da ya nuna amfanin yin azumi na wucin gadi ga masu ciwon sukari, inda suka kara da cewa dole a kula sosai wajen ba da shawarar yin sa ba tare da duba yanayin lafiyar kowane majinyaci ba.

A cewar Dr. Olopade, ya zama dole masu ciwon sukari na 2 su tattauna batun azuminsu da likitocinsu domin kada rashin lafiyarsu ya kara tabarbarewa saboda rashin daidaita magungunansu a lokacin azumin.

Kara karanta wannan

ASUU ta magantu kan sabuwar N1trn da ake yadawa tana bukata daga FG

Ya ce:
“Ya kamata mutanen da ke da ciwon sukari na 2 sannan suke fatan yin azumin addinin su tattauna shirye-shiryen azuminsu da likitocinsu domin a daidaita magungunansu ta yadda zai yi daidai da ka’ida.
“Manufar shine a cimma yarjejeniyar da ba za ta yi musu lahani ba, ta yadda za su kiyaye imaninsu da al’adunsu.
“Majinyatana, wanda yawancinsu Musulmai ne suna tattauna muradinsu na son yin azumin Ramadana sannan ana daidaita magungunansu domin ya yi daidai ka'idojin da aka tsara."

Shirin Ramadan: Kamfanin BUA ya ce ba zai kara ko kobo ba a kayayyakinsa cikin Azumi

A wani labarin Shugaban kamfanin BUA, Alhaji Abdulsamad Isyaku Rabiu, ya yiwa yan Najeriya alkawarin cewa kamfanin ba zai kara farashin kayayyakinsa ba a yanzu ko kuma a lokacin Ramadana.

Wakilin BUA a yankin arewacin kasar, Alhaji Muhammadu Adakawa, ya bayyana hakan a yayin wani taron manema labarai da aka yi a Kano don magance batun karin kudin kayayyaki da wasu kamfanoni suka yi a kwanan nan, Daily Trust ta rahoto.

Kara karanta wannan

El-Rufai ya fallasa alakar da gwamnati ta gano tsakanin 'yan sanda, sojoji da 'yan bindigan Najeriya

Asali: Legit.ng

Online view pixel