Shirin Ramadan: Kamfanin BUA ya ce ba zai kara ko kobo ba a kayayyakinsa cikin Azumi

Shirin Ramadan: Kamfanin BUA ya ce ba zai kara ko kobo ba a kayayyakinsa cikin Azumi

  • Shugaban kamfanin BUA, Alhaji Abdulsamad Isyaku Rabiu, ya sha alwashin cewa ba zai kara ko kobo ba a kayayyakinsa a lokacin azumin Ramadana
  • Ya bayyana hakan ne ta hannun Wakilin BUA a yankin arewacin kasar, Alhaji Muhammadu Adakawa, a yayin wani taron manema labarai
  • Alhaji Adakawa ya kuma bayar da tabbacin cewa ba za su bi sahun kamfanonin da suka kara N1500 kan buhun sikari a kwanan nan ba

Kano - Shugaban kamfanin BUA, Alhaji Abdulsamad Isyaku Rabiu, ya yiwa yan Najeriya alkawarin cewa kamfanin ba zai kara farashin kayayyakinsa ba a yanzu ko kuma a lokacin Ramadana.

Wakilin BUA a yankin arewacin kasar, Alhaji Muhammadu Adakawa, ya bayyana hakan a yayin wani taron manema labarai da aka yi a Kano don magance batun karin kudin kayayyaki da wasu kamfanoni suka yi a kwanan nan, Daily Trust ta rahoto.

Kara karanta wannan

Ango Abdullahi: Dalilin da yasa bana goyon bayan tsarin karba-karba tsakanin shiyyoyi

Shirin Ramadan: Kamfanin BUA ya ce ba zai kara ko kobo ba a kayayyakinsa cikin Azumi
Shirin Ramadan: Kamfanin BUA ya ce ba zai kara ko kobo ba a kayayyakinsa cikin Azumi Hoto: dailytrust.com
Asali: UGC

Ya ce shugaban kamfanin ya bukace shi da ya fada ma yan Najeriya cewa za su ci gaba da kiyaye farashin da suke sayar da kayayyakinsu a yanzu har bayan watan azumin Ramadana mai kamawa.

Alhaji Adakawa ya kuma bayyana cewa a kwanan nan wasu kamfanoni sun aiwatar da karin N1500 kan kowani buhun 50kg na sikari amma ya bayar da tabbacin cewa BUA ba zai bi sahunsu ba.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ya yi alkawarin samar da isassun kayan da za su dauke samun karancin kayan masarufi da ke haddasa tashin farashin kayayyaki, rahoton Vanguard.

Ya ce:

“A wannan shekarar, hukumar kamfani BUA yana ganin yana muhimmanci ya saurara da amsa rokon abokan cinikinsa cewa kada ya bi sahun saura wajen yin karin farashin kayayyakinsa, musamman sikari.

“Don haka, hukumar ta umurce ni da in sanar da jama’a cewa ba za ta kara farashin kayanta ba a yanzu da kuma lokacin Ramadan.”

Kara karanta wannan

Rikicin Masarautar Kano da Kamfanin jirgi: Ya kamata manya su saka baki, inji wata kungiya

Ribar N1000: Kamfanin BUA ya tona asirin 'yan kasuwa, ya ce sune silar tsadar siminti

A gefe guda, wani rahoton Daily Trust ya bayyana cewa, kamfanin simintin BUA ya ta'allaka ci gaba da hauhawar farashin siminti a kasar ga 'yan kasuwa da ke cin kazamin riba fiye da kima a harkallar siminti a kasar.

Kamfanin ya zargi 'yan kasuwa da taka rawar gani wajen ganin farashin siminti bai sauko ba a Najeriya, lamarin da 'yan Najeriya ke ci gaba da kokawa a kai.

Shugaban kamfanin, Abdul Samad Rabiu ne ya bayyana haka a lokacin da ya gana da manema labarai a fadar shugaban kasa bayan ya ziyartar shugaban kasa Muhammadu Buhari a fadar shugaban kasa da ke Abuja.

Asali: Legit.ng

Online view pixel