Babban rashi: Allah ya yiwa mahaifin ministan Buhari rasuwa

Babban rashi: Allah ya yiwa mahaifin ministan Buhari rasuwa

  • Mahaifin karamin ministan kwadago da daukar ma’aikata, Olorogun Festus Keyamo, ya rigamu gidan gaskiya
  • Pa keyamo ya mutu ne a ranar Asabar, 5 ga watan Maris, a jihar Delta, yana da shekaru 83 a duniya
  • Hadimin labaran ministan, Tunde Moshood, ne ya sanar da labarin mutuwar a cikin wata sanarwa da ya fitar

Delta - Karamin ministan kwadago da daukar ma’aikata, Olorogun Festus Keyamo, ya yi babban rashi na mahaifin, Pa Mathias Keyamo.

Pa keyamo ya mutu a ranar Asabar, 5 ga watan Maris, a Effurun da ke karamar hukumar Uvwie na jihar Delta. Ya mutu yana da shekaru 83 a duniya, Vanguard ta rahoto.

Babban rashi: Allah ya yiwa mahaifin ministan Buhari rasuwa
Babban rashi: Allah ya yiwa mahaifin ministan Buhari rasuwa Hoto: guardian.ng
Asali: Facebook

Da ake sanar da labarin mutuwar a cikin wata sanarwa dauke da sa hannun hadimin labaran ministan, Tunde Moshood, ya ce:

Kara karanta wannan

Dirama a Kotu: Saurayin da ake zargi da kashe budurwarsa ya koma mawaƙi da ya ga shaidu

"An haifi Pa Keyamo a ranar 23 ga watan Agustan 1938, a kwatas din Erovie da ke Effurun, jihar Delta.
"Pa Mathias Keyamo ya taso a Kaduna da Ilaro, jihar Ogun inda ya hadu sannan ya auri matarsa, Misis Caroline Keyamo (nee Ogunjobi).
"Nan take sai suka koma Ughelli da ke jihar Delta inda ya fara haifan dukka yaransa, ciki harda karamin ministan kwadago da daukar ma’aikata, Olorogun Festus Keyamo, SAN.”

Rahoton ya kuma kawo cewa iyalan za su sanar da shirye-shiryen binnesa nan gaba kadan.

Allah ya yiwa Diraktan agajin kungiyar Izala na Nasarawa, rasuwa

A wani labarin, mun ji cewa Allah ya yiwa Diraktan Agaji na kungiyar Izalatul Bid’ah wa iqaamatus Sunnah JIBWIS na jihar Nasarawa, Alhaji ALiyu Umar Bawa, rasuwa.

Kara karanta wannan

Babban dalilin da yasa na fara daukan bindiga, Bello Turji a zantawarsa da yan jarida

Kungiyar Izalah ta sanar da hakan ne a shafinta na Facebook inda shugaban kungiyar na kasa, Sheikh Abdullahi Bala Lau, yayi ta’aziyya.

An bayyana cewa marigayi Alhaji Bawa ya mutu ne sakamakon hadarin mota data rutsa da shi a hanyar Lafia zuwa Akwanga a jihar Nasarawa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel