Allah ya yiwa Diraktan agajin kungiyar Izala na Nasarawa, rasuwa

Allah ya yiwa Diraktan agajin kungiyar Izala na Nasarawa, rasuwa

  • Shugaban kungiyar addinin ta Izala ya aike sakon ta'aziyyarsa kan rashin Dirakta Izalah na Nasarawa
  • Kwamandan ya rasu ne sakamkon hadarin mota a hanyar Nasarawa kuma ya samu raunuka
  • Bayan kwanaki biyu yana jinyan raunukan Allah ya karbi rayuwarsa

Birnin tarayya Abuja - Allah ya yiwa Diraktan Agaji na kungiyar Izalatul Bid’ah wa iqaamatus Sunnah JIBWIS na jihar Nasarawa, Alhaji ALiyu Umar Bawa, rasuwa.

Kungiyar Izalah ta sanar da hakan ne a shafinta na Facebook inda shugaban kungiyar na kasa, Sheikh Abdullahi Bala Lau, yayi ta’aziyya.

An bayyana cewa marigayi Alhaji Bawa ya mutu ne sakamakon hadarin mota data rutsa da shi a hanyar Lafia zuwa Akwanga a jihar Nasarawa.

Ya kara da cewa marigayin yayi jinya na kwana biyu kafin nan Allah ya masa rasuwa.

Kara karanta wannan

Yadda matan Gwamnoni su ka fusata mutane da suka kai wa Aisha Buhari ‘cake’ har Dubai

Tuni aka masa janaza kamar yadda shari’ar musulunci ta tsara a safiyar larabar nan.

Allah ya yiwa Diraktan agajin kungiyar Izala na Nasarawa, rasuwa
Allah ya yiwa Diraktan agajin kungiyar Izala na Nasarawa, rasuwa
Asali: Facebook

Yace:

Innalillahi wa inna ilaihi raji’un!!!

“Bamu San komi akan marigayin ba illa alkhairan sa, ya kare rayuwar sa baki daya wajen hidimtawa addini. Muna addu’ar Allah ya jikansa ya masa rahama ya hadamu a jannatul firdausi baki dayan mu, ya kiyaye masa iyalansa“ Inji shugaban JIBWIS Sheikh Abdullahi Bala Lau.

Allah ya jikansa da rahama. Amin.

Kwamandan ya rasu ne sakamakon hadarin mota a hanyar Nasarawa kuma ya samu raunuka

Asali: Legit.ng

Online view pixel