Babban dalilin da yasa na fara daukan bindiga, Bello Turji a zantawarsa da yan jarida

Babban dalilin da yasa na fara daukan bindiga, Bello Turji a zantawarsa da yan jarida

  • Tun bayan haduwa da Sheikh Ahmad Gumi, Bello Turji ya sake fitowa haduwa da yan jarida
  • Turji ya ce abinda idanuwansa ke gani na rashin adalcin da akewa Fulani ya tilasta masa daukar bindiga
  • Arewacin Najeriya har ila yau na fama da ta'addancin yan bindiga masu garkuwa da mutane

Zamfara - Barandanci, ta'addanci, garkuwa da mutane sun zama ruwan dare a Arewacin Najeriya musamman yankin Arewa maso yamma.

Jihohin dake fama da matsalar yan bindiga sun hada da Zamfara, Katsina, Sokoto, Kaduna, da Neja.

A jihar Zamfara kadai, an raba mutane akalla 785,000 da muhallansu.

Tashar Trust TV ta zanta da kasurgumin jagoran yan bindiga Bello Turji, inda ya bayyana dalilin da yasa ya dau bindiga ya fara ta'addanci.

A cewarsa, rashin adalcin da akewa Fulani ya tilasta masa daukar bindiga.

Kara karanta wannan

Da Dumi-Dumi: Yan Bindiga Sun Yayan Shahararren Jarumin Fina-Finan Najeriya

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Bello Turji
Babban dalilin da yasa na fara daukan bindiga, Bello Turji a zantawarsa da yan jarida
Asali: Facebook

A hirar, ya bayyana cewa a kasuwar Shinkafi ya fara ganin yadda aka yiwa dan Adam yankan rago.

Yace jami'an Yan Sa Kai suka kawo wani mutumi kusa da kwatan Shinkafi kuma suka yi masa yankan rago a bainar jama'a.

Turji yace dole tasa makiyaya suka fara daukar bindiga don kare kawunansu saboda an hanasu shiga garin Shinkafi a jihar Zamfara.

TrustTV zata haska hirar misalin karfe 8 na daren Asabar.

Jami'an tsaro sun kashe 'yan ta'adda sama da 200 a wata jahar arewa

A bangare guda, Jami’an tsaro a jihar Neja sun kashe yan ta’adda sama da guda 200 a cikin kwanaki hudu da suka gabata.

The Nation ta rahoto cewa an kashe yan ta’addan ne a kananan hukumomin Mariga, Wushishi, Mokwa da Lavun.

Kwamishinan kananan hukumomi, harkokin sarauta da tsaron cikin gida, Emmanuel Umar, wanda ya bayyana hakan a yayin wani taro kan lamarin tsaro a jihar ya ce kungiyoyin yan bindiga hudu na ta kai farmaki a jihar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel