Wata Amarya Ta Janyo Cece-Cece Kuce Bayan Ta Wankawa Mijinta Mari Lokacin Daurin Aurensu

Wata Amarya Ta Janyo Cece-Cece Kuce Bayan Ta Wankawa Mijinta Mari Lokacin Daurin Aurensu

  • Wata mata ta fusata tta ware ta yankawa mijinta mari lokacin da ake tsaka da daura aurensu
  • Bidiyon auren Mehdi Shadan ya yadu sosai yayin da aka ga mutumin yana rama marin da amaryarsa tai masa
  • Akalla sama da mutum dubu 92 ne suka kalli bidiyon yayin da ya baiwa wasu masu amfani da Twitter mamaki.

Bidiyon wasu ma'aurata da suka yi fada a ranar aurensu ya samu ra'ayi sama da 92k a shafin Twitter kadai.

Wani mai amfani da Twitter, Mehdi Shadan , ya wallafa wani bidiyo a ranar 12 ga Disamba. A cikin faifan faifan, an ga ma'auratan suna gasar mari.

A cikin gajeren faifan bidiyon da ya dauki tsawon dakika 19 kacal, amaryar ce ta fara marin mutumin yayin da duk wanda suke wurin suka cika da mamakin abin da ta yi.

Kara karanta wannan

Mai Sayar da Kayan Marmari Yaki Karban Sabon Kudin Da CBN Ya Fito Dashi, Yace Jabu Ne

Maaurata
Wata Amarya Ta Janyo Cece-Cece Kuce Bayan Ta Wankawa Mijinta Mari Lokacin Daurin Aurensu
Asali: UGC

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Bidiyon wasu ma'aurata suna fada a ranar aurensu

Dangane da abin da ya jawo wannan zafafan mari, da alama angon ne ya ke kokarin dole sai ya ciyar da amarya abincin biki da karfi sai ta yi kokarin hana shi.

Ta mari angonta sai ya mare ta shima ya rama, daganann sai hankalin masu bikin suka juya kansu.

An Halice Mu Ne Dan Junanmu

Mutanen da ke wurin sun garzaya don raba fadan yayin da ma'auratan suka kacame.

Ana kokarin raba fadan aka cirewa mutumin rigar wanda hakan yasa fadan sake yin kamari.

Bidiyon ya baiwa masu amfani da Twitter mamaki.

A cikin martani, wani mai amfani da aka bayyana a matsayin

@tbhnikhil ya ce:

"kun ji dadin junan ku."

Kara karanta wannan

Wani Miji Ya Maka Matarsa Wajen 'Yan Sanda Kan Kasa Bayanin Yadda Ta Kashe N5m Da Ya Bata

Har yanzu dai ba a san takamaimai a inda abin ya faru ba, amma zaku iya kallon bidiyon a nan.

Wani Mutum Ya Fusata Ya fasa Yin Aure, A Ranar Daurin Aurensa. Bidiyon Ya Yadu A TikTok

A wani labarin makamancin haka, Legit.ng ta ruwaito cewa, wani magidanci ya fasa aure kuma ya bar wurin daurin auren.

An bayyana cewalokacin da aka fara bikin aure a lokacin aka ga mutumin na daure fuska.

A cewar mutumin, ya gano cewa amaryar tasa ta kai wa tsohon saurayin nata ziyara a mintunan karshe, lamarin da ya bata masa rai.

Mutumin ya kutsa kai wajen daurin auren, sai amaryar da sauran 'yan biki suka bi shi suna rokonsa.

Mutumin ya ki sauraren amaryar duk da ta fadi kasa dan ya gafartamata amma yaki

Asali: Legit.ng

Online view pixel