Budurwar da ta Tashi Saurayi a Wurin Biki Tayi Nasara, Zai yi Wuff da ita

Budurwar da ta Tashi Saurayi a Wurin Biki Tayi Nasara, Zai yi Wuff da ita

  • Karaurawar auren wata mata na kadawa, wacce aka sanya ranar aurenta da wani mutumi da ta hadu dashi wa wani biki
  • A wani bidiyo da Oyinda ta wallafa a TikTok ya bayyana yadda wani mutumi ya durkusa kasa ya nemi aurenta cikin siga irin ta soyayya
  • Oyinda ta ce ta kosa ta karasa rayuwarta da masoyinta abun kaunarta, yayin da mutane suke ta mata sambarka

Wata mata da ta wallafa wani bidiyo a dandalin TikTok wanda ke bayyana lokacin da ta amsa soyayyar wani mutumi bayan ya bukaci hakan.

Budurwa
Budurwar da ta Tashi Saurayi a Wurin Biki Tayi Nasara, Zai yi Wuff da ita. Hoto daga TikTok/@oyinakinyera
Asali: UGC

Bidiyon da budurwar mai suna Oyinda ta wallafa wacce ta ce ta hadu da mijin da zata aura a wajen liyafar biki ne. Oyinda ta ce ta hadu da mutumin ne a wajen shagalin wani biki, wanda bayan shekaru uku suka fara shirin angwancewa.

Kara karanta wannan

Budurwa ta Kwace Motar da ba Saurayinta bayan Shekatu 2 da Suka Rabu, Kazantar da ta Gani Ciki ta Tada Hankali

Sai dai, a lokacin da ta hadu dashi wajen shagalin wani biki, sai ta gane ta san shi a makaranta. Amma suka rabu, sai bayan shekaru uku, mutumin ya bayyanar mata cikin wata irin siga ta so da alamu su kadai ne a wurin.

A bidiyon da ya dauki dakiku 20, mutumin ya duka kasa don rokonta idan ta amince ta auresa yayin da ita kuma ta mika hannunta don amsar zabe.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Oyinda tayi karkashin bidiyon:

"Wasu kwanaki da suka wuce, masoyina ya tambaye ni ko zan amince in zama matarsa, inda na ce me zai hana!!! Na kosa in karshe rayuwara dashi. Ubangiji baya kuskure!"

Jama’a sun yi martani

Ba tare da jinkiri ba, masu amfani da dandalin TikTok suka fara rige-rigen zuwa sashin tsokacin bidiyon don tofa albarkacin bakunansu.

Kara karanta wannan

Wata Mata Ta Gano Mijinta Ya Yi Amarya a Ɓoye Har Sun Haihu, Ta Je Gidan An Buga Dirama a Bidiyo

@Kulola Lynn ta ce:

"Naji dadin yadda kike sanye da takalmin soso. Ina taya ku murna!"

@phartty tayi tsokaci:

"Ina taya ku murna 'yar uwa." "soyayya da dadi."

@_wanjiku_mbugua ya ce:

"Dakata ina kyan da amaryar ke da shi."

@sparte_mandloe ya ce:

"Naji dadin ganinki sanye da takalmin soso. Ina taya ku murna."

#Katy Katy tayi martani:

”Da ban mamaki yadda hakan ya faru. Ina taya ki murna."

@emissa61 ta ce:

“Oga ni fa mamata na takuramin. Na rantse ba zan amsa kiran ba. Sai naje bukukuwa da dama na wata shekarar."

Asali: Legit.ng

Online view pixel