Ba Zan Iya Cigaba Da Yin Karɓa-Karɓar Matata Da Hedimastan Makarantar Da Ta Ke Aiki Ba, Magidanci Ga Kotu

Ba Zan Iya Cigaba Da Yin Karɓa-Karɓar Matata Da Hedimastan Makarantar Da Ta Ke Aiki Ba, Magidanci Ga Kotu

  • Wani magidanci mai suna Stephen Oyediran ya yi karar matarsa a kotu yana rokon a raba aurensu na shekaru takwas
  • Oyediran ya yi ikirarin cewa matara Busayo tana bin mazaje ciki har da hedimastan makarantar da ta ke aiki kuma ya gaji da karba-karba
  • Matar, Busayo ta karyata zargin da Oyediran ya yi tana mai cewa dama tun farko ya cika zargi sannan baya kula wa da ita da yaransu

Oyo - Wani ma'aikacin kamfani, Stephen Oyediran, ya shaida wa wata kotu da ke zamanta a Mapo, Ibadan cewa yana son a raba aurensu na shekaru takwas da matarsa Busayo, kan zargin cin amanar aure.

Mr Oyediran, wanda ke zaune a Challenge, Ibadan, ya ce ya cimma matsayar rabuwa da Busayo ne saboda halinta na rashin da'a a kirki, rahoton Daily Nigerian.

Kara karanta wannan

Da Dumi-Dumi: Matar makashin Hanifa Abubakar ta juya masa baya a Kotu, ta faɗi gaskiyar lamari

Ba Zan Iya Cigaba Da Yin Karɓa-Karɓar Matata Da Hedimastan Makarantar Da Ta Ke Aiki Ba, Magidanci Ga Kotu
Na Hakura, Ba Zan Iya Cigaba Da Yin Karɓa-Karɓar Matata Da Hedimastan Makarantar Da Ta Ke Aiki Ba, Magidanci Ga Kotu. Hoto: Daily Trust
Asali: UGC

"Bayan Busayo ta amince za ta aure ni a Ondo, ban taba sanin tana bin mazaje ba.
"Da ta tare a gida na, na lura tana rayuwa irin ta kasaita kuma bata min biyayya.
"Bugu da kari, kullum tana nema daman zuwa Ondo domin ta hadu da kwarton ta," Oyediran ya shaida wa kotu.

Ya kara da cewa ya gano sakon soyayya a wayarta tsakaninta da kwartonta.

Na kuma gano tana lalata da hedimastan makarantarsu, Oyediran

Oyediran ya cigaba da cewa:

"Bugu da kari, na gano tana lalata da hedimastan makarantar da ta ke koyarwa a yanzu a Ibadan.
"Da na ga ba zan iya jure abin kunyan ba, na fada wa hedimastan ya rike Busayo kuma ya su kyalle min 'ya'ya na uku in kula da su.

Kara karanta wannan

Siyasar 2023 ta matasa ce: Ni fa ba tsoho bane, ni matashi ne mai jini a jika, inji Tinubu

"Wannan shine dalilin da yasa hedimastan ya saka aka kama ni.
"Daga bisani Busoyo ta kama hayan gida kusa da gidan hedimastan.
"Da dan alabashi da na ke samu, ina iya kokari na in kula da ita da yaran mu."

Martanin Busayo kan zargin da Oyediran ya mata

A jawabinta, Busayo ta shaida wa kotu cewa mijin ta ya dade yana zarginta duk da rashin sauke hakkinsa da baya yi.

Ta ce da farko ya musanta cewa shine mahaifin dansu na farko, daga baya ya bata hakuri suka cigaba da zama kuma baya biyan kudin makarantar yara da wasu abubuwan.

Abin da alkali ya yanke

S.M. Akintayo, alkalin kotun ya dage cigaba da sauraron shari'ar zuwa ranar 18 ga watan Maris bayan ya saurari bangarorin biyu.

Ya umurci su zauna lafiya a dukkan lokuta.

A raba mu, ya ce na cika mugun ci, har rufe kicin yake yi da dare, Firdausi ta yi karar mijinta Haruna a kotu

Kara karanta wannan

2023: El-Rufai ya magantu kan kudirin takarar shugaban kasa, ya bayyana wanda zai marawa baya

A wani labarin daban, wata Firdausi Sulaiman mai shekaru 23 ta maka mijin ta, Haruna Haruna a gaban kotun musulunci da ke zama a Magajin Gari a Kaduna tana bukatar a raba auren su da shi saboda yadda yake dukanta kamar gangar tashe sakamakon mungun cin abincin ta.

Kamar yadda NewsWireNGR ta bayyana, a korafin da ta yi wa Kotu, Firdausi wacce take zama a Rigasa dake Kaduna ta ce har rufe kicin Haruna yake yi da dare.

Alkalin kotun, Nuhu Falalu, bayan sauraron bangarorin guda biyu, ya dage sauraron shari’ar har sai ranar 4 ga watan Oktoba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel