Da dumi-dumi: Shugaba Buhari ya dawo gida Abuja maimakon birnin Landan

Da dumi-dumi: Shugaba Buhari ya dawo gida Abuja maimakon birnin Landan

  • Shugaba Muhammadu Buhari ya dawo Abuja bayan halartan taron UN a birnin Nairobi na kasar Kenya
  • Hadimin shugaban kasar, Bashir Ahmad ne ya sanar da batun dawowar nasa a yau Juma'a, 4 ga watan Maris
  • Buhari ya dawo kasar ne a daidai lokacin da ake ta sa ran zai tafi Landan ganin Likitocinsa na tsawon makonni biyu

Abuja - Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya dawo babbar birnin tarayya Abuja bayan ya halarci wani taro a babbar birnin Nairobi, kasar Kenya.

A ranar Litinin ne jirgin Buhari ya lula birnin Nairobi domin halartan taron cikar shirin majalisar dinkin duniya na yanayi (UNEP) shekaru 50 da kafuwa.

Da dumi-dumi: Shugaba Buhari ya dawo gida Abuja maimakon birnin Landan
Shugaba Buhari ya dawo gida Abuja maimakon birnin Landan Hoto: Premium Times
Asali: Facebook

Mai ba shugaban kasa shawara kan shafukan sadarwa na zamani, Bashir Ahmad ne ya sanar da batun dawowar shugaban kasa a cikin wata sanarwa da ya fitar a shafinsa na Twitter a ranar Juma’a, 4 ga watan Fabrairu.

Kara karanta wannan

Yanzu-yanzu: Shugaba Buhari zai tafi birnin Landan ganin Likita na tsawon makonni 2

Ya rubuta a shafin nasa:

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

"Shugaban kasa Muhamnmadu Buhari ya dawo Abuja, bayan halartan taron cikar shirin UN na yanayi (UNEP) shekaru 50 a Nairobi, Kenya."

Ana ta sa ran Buhari zai tafi birnin Landan ganin Likita na tsawon makonni 2

Dawowar shugaban kasar ya bayar da mamaki domin ana ta sa ran zai tafi Landan, don ganin Likitocinsa na tsawon makonni biyu bayan halartan taron na UN.

Harma mai magana da yawun Shugaban kasa, Femi Adesina, ya tabbatar da hakan a jawabin da ya saki ranar Talata.

Buhari Ya Naɗa Magajin Farfesa Sulaiman Bogoro A TETFund

A wani labarin, Buhari ya amince da nadin Arc S.T. Echono a matsayin sabon shugaban hukumar bayar da tallafi ga manyan makarantu ta Najeriya wato TETFUND.

Echono, tsohon sakataren dindindin na ma'aikatar ilimi, zai maye gurbin Farfesa Sulaiman Elias Bogoro ne, wanda wa'adinsa na shekara biyar zai kare a ranar 18 ga watan Maris na 2022, rahoton Daily Trust.

Kara karanta wannan

Babu shugaba da mataimaki a kasa: Osinbajo ya keta hazo bayan shillawar Buhari Faris

Asali: Legit.ng

Online view pixel