Babu shugaba da mataimaki a kasa: Osinbajo ya keta hazo bayan shillawar Buhari Faris

Babu shugaba da mataimaki a kasa: Osinbajo ya keta hazo bayan shillawar Buhari Faris

  • Kamar dai shugaban kasa Muhammadu Buhari, mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo a ranar Lahadi, 27 ga watan Fabrairu ya bar fadar shugaban kasa da ke Abuja
  • Osinbajo zai halarci taron bude wata kotun kare hakkin dan Adam da jama'a ta Afrika ne a birnin Arusha na kasar Tanzania
  • Mataimakin shugaban kasar zai yi magana ne a matsayin bako mai jawabi a wurin taron, inda zai tattauna kan maudu'in The African Court, The Africa We Want

Mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo a ranar Lahadi, 27 ga watan Fabrairu, ya bar Najeriya zuwa Arusha na kasar Tanzaniya domin halartar taron 2022 na bude kotun kare hakkin dan Adam da jama'a ta Afrika.

Mai taimaka wa Osinbajo kan harkokin yada labarai, Laolu Akande ne ya sanar da hakan ta shafinsa na Twitter ranar Lahadi.

Kara karanta wannan

An shiga tsakani: Za a yi tattaunawar zaman lafiya tsakanin Ukraine da Rasha yau Litinin

Farfesa Yemi Osinbajo ya shilla kasar waje
Babu shugaba da mataimaki a kasa: Osinbajo ya keta hazo bayan shillawar Buhari Faris | Hoto: Laolu Akande
Asali: Twitter

Akande ya bayyana cewa ana sa ran Osinbajo wanda zai kasance bako mai jawabi a babban taron zai yi magana a kan maudu'in The African Court, The Africa We Want; wato Kotun Afirka, Afirka da Muke So.

Hadimin na Osinbajo ya kara da cewa, ubangidan nasa zai yi ganawa da takwarorinsa na kasashen nahiyar Afrika.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Rubutunsa na Twitter ya bayyana cewa:

"A yau ne mataimakin shugaban kasa zai bar Abuja zuwa Arusha na kasar Tanzaniya domin halartar bikin bude kotun kare hakkin bil'adama da kare hakkin jama'a na Afrika na shekarar 2022 a matsayin babban bako a gobe."
"Zai yi magana ne kan THE AFRICAN COURT & THE AFRICA WE WANT, zai kuma gudanar da taro da takwarorinsa daga kasashe biyu."

Ana tsaka da yakin Rasha da Ukraine, Shugaba Buhari ya fice Najeriya, ya nufi Turai

Kara karanta wannan

Da dumi-dumi: Belarus ta shiga yakin Rasha, tana shirin danna dakarunta cikin Ukraine

A wani labarin, a ranar 26 ga watan Fabrairu, 2022, shugaban kasa, Muhammadu Buhari, ya dira Faris, babban birnin kasar Faransa, domin fara ziyarar aiki ta mako biyu.

A rahoton da TVC News ta tattaro, Jirgin shugaba Buhari ya ɗira a filin sauka da tashin jiragen sama na Le Bourget da misalin ƙarfe 7:45 na daren ranar Asabar.

A cikin ziyarar mako biyu, Ana tsammanin shugaban ƙasan zai halarci taron zaman lafiya na kwana uku da aka shirya gudanarwa daga ranar Jumu'a 11 ga watan Maris, zuwa Lahadi 13 ga watan Maris.

Asali: Legit.ng

Online view pixel