Ba zai yiwu ba: Majalisa ta yi watsi da kudurin hana jami'an gwamnati tura 'ya'yansu karatu waje

Ba zai yiwu ba: Majalisa ta yi watsi da kudurin hana jami'an gwamnati tura 'ya'yansu karatu waje

  • A ranar Alhamis ne Majalisar Wakilan Najeriya ta kada kuri’ar kin amincewa da kudurin dokar hana jami’an gwamnati tura ‘ya’yansu karatu kasashen waje
  • ‘Yan majalisar dai sun ce kudurin dokar ya saba wa muhimman hakkokin jami’an gwamnati tare da nuna musu wariya, hakan yasa suka yi watsi da ita bayan a karatu na uku
  • Dan majalisa Sergius Ogun ne ya dauki nauyin kudirin dokar wanda ya taba yin kira da a haramtawa jami’an gwamnati zuwa kasar waje jinya

FCT, Abuja - ‘Yan majalisar wakilai a ranar Alhamis, 3 ga watan Maris, sun yi watsi da kudirin dokar da ke neman hana jami’an gwamnati tura ‘ya’yansu makaranta zuwa kasashen ketare.

Wasu daga cikinsu sun dage kan cewa hakan ya saba wa muhimman hakkokin ‘yan Najeriya.

Majalisar wakilai ta yi watsi da kudurin da ke neman hana jami'an gwamnati tura 'ya'yansu karatu waje
Ba zai yiwu ba: Majalisa ta yi watsi da kudurin hana jami'an gwamnati tura 'ya'yansu karatu waje | Hoto: dailynigerian.com
Asali: UGC

Kudirin dokar na Sergius Ogun, ya nemi a tabbatar da cewa jami’an gwamnatin da za su iya nuna cewa za su iya daukar nauyin ‘ya’yansu a kasashen waje ba tare da amfani da kudin gwamnati ba ne kadai za su iya hakan, a cewar Channels TV.

Kara karanta wannan

Hadimin Buhari: Zaben 2023 zai fi kowane zabe zama sahihi saboda kokarin Buhari

Yadda kada kuri'ar ta kasance

‘Yan majalisar sun roki Mista Ogun da ya janye kudirin amma ya ki, kuma da aka kada kuri’a, sai akasarin kuri’un suka nuna kin amincewa da kudirin.

Daga karshe, kudurin da ke neman sauya sashe na 46 a kundin kiwon lafiya ya sha kaye a majalisa bayan dogon caccaka tsinke daga nan aka yi watsi da ita, kamar yadda Daily Nigerian ta ruwaito.

Shehu Sani: Idan da matan gwamnoni basu shilla kasar waje ba, da majalisa bata yi waje da kudurin mata ba

A wani labarin, tsohon sanatan da ya wakilci Kaduna ta tsakiya, Shehu Sani ya bayyana cewa da ace matan gwamnonin jihohi 36 na Najeriya da sauran matan da ke fada aji sun mayar da hankali wajen tattaunawa game da kudirin mata a majalisar dokokin kasar, da an samu sakamako mai kyau.

Kara karanta wannan

Sanusi II: Abu 1 da ya sa Jonathan da Ganduje suka tsige ni daga CBN da sarautar Kano

Hakan na zuwa ne a yayin da ake tsaka da neman a karawa matan Najeriya yawan kujeru a majalisun dokokin tarayya da na jiha.

A ranar Laraba ne kungiyoyin mata suka gudanar da zanga-zanga a majalisar dokoki biyo bayan watsi da kudirin mata da yan majalisar suka yi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel