Shehu Sani: Idan da matan gwamnoni basu shilla kasar waje ba, da majalisa bata yi waje da kudurin mata ba

Shehu Sani: Idan da matan gwamnoni basu shilla kasar waje ba, da majalisa bata yi waje da kudurin mata ba

  • Sanata Shehu Sani ya yi martani a kan kudirin jinsin mata da majalisar dokokin tarayya ta yi watsi da shi
  • Sani ya ce da ace matan gwamnoni da manyan mata masu fada aji basu tafi kasar waje ba da majalisa bata yi waje da kudirin ba
  • Hakan na zuwa ne a daidai lokacin da ake cece-kuce bayan bayyanar bidiyon matan gwamnoni suna gabatarwa Aisha Buhari da kek din zagayowar ranar haihuwa a Dubai

Tsohon sanatan da ya wakilci Kaduna ta tsakiya, Shehu Sani ya bayyana cewa da ace matan gwamnonin jihohi 36 na Najeriya da sauran matan da ke fada aji sun mayar da hankali wajen tattaunawa game da kudirin mata a majalisar dokokin kasar, da an samu sakamako mai kyau.

Hakan na zuwa ne a yayin da ake tsaka da neman a karawa matan Najeriya yawan kujeru a majalisun dokokin tarayya da na jiha.

Kara karanta wannan

Zanga-zanga: Mata sun tare kofar majalisa saboda kin amincewa da wani kudirin mata

Shehu Sani: Idan da matan gwamnoni basu shilla kasar waje ba, da majalisa bata yi waje da kudurin mata ba
Shehu Sani ya ce idan da matan gwamnoni basu tafi kasar waje ba, da majalisa bata yi waje da kudurin mata ba
Asali: UGC

A ranar Laraba ne kungiyoyin mata suka gudanar da zanga-zanga a majalisar dokoki biyo bayan watsi da kudirin mata da yan majalisar suka yi.

A wani wallafa da ya yi a shafinsa na Twitter a ranar Alhamis, 3 ga watan Maris, Shehu Sani ya ce:

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

“Idan da ace matan gwamnoni 36 na kasar da matan da ke rike da manyan mukaman gwamnati, na ma’aikatu masu zaman kansu da kungiyoyin jama’a sun sanya ido 24/7 a majalisar dokokin tarayya a yayin tsara kudirin, da sun samu abin da suke so. Da yawa daga cikinsu basa a kasar kuma sun rasa damar.”

A ranar Laraba ne wani bidiyo ya dunga yawo a shafukan sadarwa na matan gwamnoni yayin da suke gabatar da ‘kek’ din zagayowar ranar haihuwa ga Aisha Buhari a kasar Dubai.

Kara karanta wannan

Babu dadi: IGP ya koka kan yadda 'yan sanda ke amfani da makamai ta wasu hanyoyi

Jim kadan bayan bidiyon ya yadu a yanar gizo, an yada jita-jitar cewa matan gwamnonin Najeriya sun wanki kafa zuwa Dubai musamman don gabatar wa matar shugaban kasan kek da kudin masu biyan haraji.

Dalilin da yasa muka yi bikin zagayowar ranar haihuwar Aisha Buhari a Dubai, Matan Gwamnoni

A gefe guda, Bisi Fayemi, shugabar kungiyar matan gwamnonin Najeriya kuma matar gwamnan jihar Ekiti, ta yi martani a kan batun ta wata takarda da ta fitar a shafinta na Twitter, inda ta musanta cewa, matan gwamnonin basu wanki kafa zuwa Dubai don gabatar wa matar shugaban kasa kek a ranar zagayowar haihuwar ta ba.

Fayemi ta bada labarin yadda suka kai ziyarar aiki a Dubai, sai yazo dai-dai da ranar zagayowar haihuwar Aisha Buhari saboda haka suka yanke shawarar yi ma ta kyautar ba-zata da kek.

Fayemi ta ce, sun yi mamakin ganin yadda aka juya ma'anar labarin bidiyon da yayi yawo a yanar gizo.

Kara karanta wannan

Garin dadi na nesa: Bidiyon gidan mai a Dubai da ake yawo da shi ya janyo cece-kuce

Asali: Legit.ng

Online view pixel