Yajin aiki a Jami'o'i: Gwamnatin Buhari ta kara zaman tattaunawa da ASUU

Yajin aiki a Jami'o'i: Gwamnatin Buhari ta kara zaman tattaunawa da ASUU

  • Gwamnatin tarayya ta koma teburin tattaunawa da kungiyar ASUU domin warware matsalolin da suka jawo yajin aiki
  • Har yanzun akwai sabani tsakanin bangarorin biyu game da tsarin da ASUU ta kawo na biyan yayanta albashi UTAS
  • Ministan kwadugo da samar da ayyukan yi, Chris Ngige, yace yana da yaƙinin za'a samu matsaya nan ba da jimawa ba

Abuja - A ranar Talata 1 ga watan Maris, 2022, gwamnatin tarayya ta koma teburin tattaunawa da kungiyar malaman jami'o'i ASUU.

Channels tv ta rahoto cewa taron na yau Talata shi ne karo na biyu tun bayan da ASUU ta sanar da tsunduma yajin aikin gargaɗi na wata ɗaya mako uku da suka gabata.

ASUU na bukatar a ƙara inganta makarantun gwamnati ta hanyar ƙara musu walwala da jin daɗi da kuma gine-gine, da sauran wasu bukatu.

Kara karanta wannan

Babu dadi: IGP ya koka kan yadda 'yan sanda ke amfani da makamai ta wasu hanyoyi

Yajin aiki a Jami'o'i
Yajin aiki a Jami'o'i: Gwamnatin Buhari ta kara zaman tattaunawa da ASUU Hoto: channelstv.com
Asali: UGC

Kungiyar malaman a taronta da FG na ranar Talata, ta bayyana cewa ba zata sake amince wa ta sanya hannu a wata yarjejeniyar fahimtar juna da gwamnati ba.

Kungiyar ta bukaci gwamnatin tarayya ta aiwatar da alkawurra da ta ɗauka a MoU da suka rattaba hannu a baya.

Shin akwai alamun kawo karshen yajin aiki?

Sa dai a bangaren gwamnati, Ministan ayyuka da samar da ayyukan yi, Dakta Chris Ngige, ya nuna kwarin guiwarsa cewa za'a warware sabanin dake tsakani ba da jimawa ba.

Kowane bangare ya ɗauki matsaya ta daban game da fara aiki da tsarin biyan albashi da ASUU ke bukatar a yi wa ƴaƴanta amfani da shi UTAS.

Yayin da ministan ke ganin laifin ASUU ne na jinkirin bin matakan da hukumar fasaha NITDA take kai, Ita kuma kungiyar na ganin NITDA ba ta shirya musu abin da ya dace ba.

Kara karanta wannan

Da-Dumi-Dumi: Lamari ya ɗau zafi, Ministan Buhari ya fice daga dakin taro da Daliban Najeriya

Saɓani game da tsarin biyan albashi na ɗaya daga cikin manyan maƙasudan da ASUU ta tsunduma wannan yajin aikin na baya, kamar yadda Daily Nigerian ta rahoto.

A wani labarin kuma Sabon mataimakin gwamna Matawalle ya yi murabus daga kujerar Sanata

Sanata Mai wakiltar jihar Zamfara ta tsakiya, Sanata Hussaini Nasiha, ya yi murabus daga kujerarsa ta majalisa a hukumance.

Jaridar Puch ta rahoto cewa ya ɗauki wannan matakin ne biyo bayan naɗa shi mataimakin gwamna da Gwamna Matawalle ya yi a Zamfara.

Asali: Legit.ng

Online view pixel