Karin bayani: Majalisa ta amince da kudurin takara ga 'yan takara masu zaman kansu

Karin bayani: Majalisa ta amince da kudurin takara ga 'yan takara masu zaman kansu

  • Majalisar dokokin Najeriya ta amince da kudurin dokar da ke neman bai wa 'yan takara masu zaman kansu damar tsayawa takara
  • Majalisar ta amince da hakan ne a zamanta na yau Talata, 01 ga watan Maris a zauren majalisar da ke Abuja
  • Hakazalika, majalisar ta kuma tattauna kan wasu kudurorin da aka gabatar a gabanta duk a yau Talata

FCT, Abuja - A yau Talata ne majalisar dattijai ta amince da kudirin doka mai lamba 58 da ke neman bai wa ‘yan takara masu zaman kansu damar tsayawa takara, The Nation ta ruwaito.

Kudurin zai shafi ‘yan takarar shugaban kasa, na gwamna, da ‘yan majalisun tarayya, da na majalisun jihohi, da na kananan hukumomi.

Sanatoci 94 ne suka yi rajistar kada kuri’a, 89 sun kada kuri’a amincewa yayin da 5 suka ki amincewa, kamar yadda Punch ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Da Duminsa: Majalisa ta yi watsi da kudurin kirkiro wa mata Kujeru na musamman, da kudirin VAT

Majalisa ta amince da dokar 'yan takara
Da dumi-dumi: Majalisa ta sanya hannu kan kudurin takara | Hoto: channelstv.com
Asali: UGC

Hakazalika, majalisar ta yi watsi da wani kudirin doka da ke neman bai wa ‘yan Najeriya mazauna kasashen waje damar kada kuri’a a lokacin zabe.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

A gefe guda, ‘yan majalisar sun ki amincewa da wani kudirin doka da ke neman samar da zaben Magajin Gari a Babban Birnin Tarayya, an samu kuri'u 62 da suka amince da hakan.

A ka'ida ana bukatar kuri'u 73 domin amincewa da kudirin.

Har ila yau, wani kudirin doka da ke neman tabbatar da cewa mutumin da ya yi rajistar zabe kuma mazaunin FCT ne zai zama Minista mai wakiltar FCT shi ma ya sha kasa a majalisar.

Sanatoci 67 ne kawai suka zabi amincewa da hakan maimakon 73 da ake bukata.

An yi gaba an dawo baya: Buhari ya nemi a soke wani sashe na sabuwar dokar zabe da ya sanyawa hannu

Kara karanta wannan

'Karin Bayani: 'Yan Majalisar Wakilai Sun Ƙi Amincewa Da Fansho Na Har Abada Ga Shugabannin NASS

A wani labarin, a yau Talata 1 ga watan Maris ne shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya bukaci majalisar dokokin kasar Najeriya da ta yi wa sabuwar dokar zabe ta 2022 da aka sanya wa hannu kwaskwarima.

A wata wasika daga fadar shugaban kasa da shugaban majalisar dattijai, Ahmad Lawan ya karanta yau Talata, shugaba Buhari ya shaidawa majalisar dokokin kasar da ta duba batun cire sashe na 84 (12) gaba daya.

Wannan bangare na dokar zabe ya tanadi doka kan masu rike da mukaman siyasa da su yi murabus daga ofishinsu kafin su yi takarar fidda gwani a jam’iyyunsu na siyasa, inji rahoton Punch.

Asali: Legit.ng

Online view pixel