An yi gaba an dawo baya: Buhari ya nemi a soke wani sashe na sabuwar dokar zabe da ya sanyawa hannu

An yi gaba an dawo baya: Buhari ya nemi a soke wani sashe na sabuwar dokar zabe da ya sanyawa hannu

  • Shugaba Buhari ya sake mika wasika ga majalisar dokokin Najeriya, ya nemi sauyi a sabuwar kudurin doka
  • Wannan na neman gyara na zuwa ne jim kadan bayan Buhari ya amince da kudurin zabe da aka gabatar
  • Buhari ya nemi a soke wani bangare na dokar, shugaban majalisa ya karanta kudurin a farfajiyar majalisa

FCT, Abuja - A yau Talata 1 ga watan Maris ne shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya bukaci majalisar dokokin kasar Najeriya da ta yi wa sabuwar dokar zabe ta 2022 da aka sanya wa hannu kwaskwarima.

A wata wasika daga fadar shugaban kasa da shugaban majalisar dattijai, Ahmad Lawan ya karanta yau Talata, shugaba Buhari ya shaidawa majalisar dokokin kasar da ta duba batun cire sashe na 84 (12) gaba daya.

Kara karanta wannan

Ranar babban taron APC na kasa na nan daram, Gwamnonin APC sun magantu

Shugaba Buhari ya nemi a sake gyara dokar zabe
An yi gaba an dawo baya: Buhari ya nemi a sake gyara wani wuri a sabuwar dokar zabe | Hoto: premiumtimesng.com
Asali: UGC

Wannan bangare na dokar zabe ya tanadi doka kan masu rike da mukaman siyasa da su yi murabus daga ofishinsu kafin su yi takarar fidda gwani a jam’iyyunsu na siyasa, inji rahoton Punch.

A cewar shugaban, tanadin dokar ta sashe na 84 (12 ) ta saba wa hakkin wadanda ke rike da madafun iko.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

'Yan Majalisar wakilai sun ki amincewa da fansho na har abada ga shugabannin NASS

Mambobin majalisar wakilai na tarayya sun ki amincewa da wata yunkuri na yin dokar biyan fansho na har abada ga shugabannin majalisar tarayya, rahoton Daily Trust.

Mambobin sun ki amincewa da kudin dokar da ya ce:

"Kudirin doka domin yin garambawul ga kundin tsarin mulkin Najeriya ta 1999 domin bada fansho na har abada ga shugabannin majalisar tarayya; da wasu abubuwa da suka shafe hakan da amincewa da su."

Kara karanta wannan

'Karin Bayani: 'Yan Majalisar Wakilai Sun Ƙi Amincewa Da Fansho Na Har Abada Ga Shugabannin NASS

Kuri'u guda 193 ne aka kada a majalisar wakilan na neman bada fansho na har abada ga shugaban majalisar dattawa da kakakin majalisar wakilai da mataimakansu, rahoton Vanguard.

Yan majalisa guda 162 sun ce a'a yayin da guda 3 ba su kada kuri'ar ba. A majalisar dattawan, Shugaban Majalisa, Ahmad Lawan ya ce:

"Kudirin dokar ba ta samu amincewa ba kwata-kwata."

Majalisun tarayya sun yi watsi da kudurin ware wa mata Kujeru, da kudirin VAT

A wani labarin, majalisar tarayya a Najeriya ta yi fatali da kudirin samar da kujeru na musamman ga mata da kuma na canza wa biyan harajin VAT wuri zuwa jerin Waje.

Daily Trust ta rahoto cewa mambobin majisar sun yi watsi da kudirorin biyu ne yayin kaɗa kuri'a kan abubuwa 68 da aka maida hankali wurin gyaran kwansutushin, ranar Talata.

A majalisar wakilan tarayya, Mambobi 209 suka kaɗa kuri'ar kin amincewa da canza wa VAT wuri, yayin da mambobi 208 suka ki amincewa da ware wa mata kujeru na musamman.

Kara karanta wannan

Zamfara: Sabon mataimakin gwamna Matawalle ya yi murabus daga kujerar Sanata

Asali: Legit.ng

Online view pixel