Zamfara: Sabon mataimakin gwamna Matawalle ya yi murabus daga kujerar Sanata

Zamfara: Sabon mataimakin gwamna Matawalle ya yi murabus daga kujerar Sanata

  • Sabon mataimakin gwamnan jihar Zamfara, Sanata Hussain Nasiha ya tura takarar murabus daga mukamin sanata zuwa Majalisa
  • Shugaban Majlaisar dattawa Sanata Ahmad Ibrahim Lawaƙ, ya karanta wasikar murabus ɗin tsohon sanatan a zaman majalisa na yau
  • Nasiha ya ɗauki wannna matakin ne domin komawa matsayin mataimakin gwamnan Zamfara, bayan tsige Mahdi Aliyu

Zamfara - Sanata Mai wakiltar jihar Zamfara ta tsakiya, Sanata Hussaini Nasiha, ya yi murabus daga kujerarsa ta majalisa a hukumance.

Jaridar Punch ta rahoto cewa ya ɗauki wannan matakin ne biyo bayan naɗa shi mataimakin gwamna da Gwamna Matawalle ya yi a Zamfara.

Mataimakin gwamnan Zamfara, Sanata Nasiha
Zamfara: Sabon mataimakin gwamna Matawalle ya yi murabus daga kujerar Sanata Hoto: Haruna Lawal Gusau/Facebook
Asali: Facebook

Nasiha ya maye gurbin, Barista Mahdi Aliyu Gusau, wanda a makon da ya gabata majalisar dokokin jihar ta tsige shi daga kan kujerarsa.

Kara karanta wannan

Muhammad Hassan Nasiha: Abubuwa 5 Da Ya Kamata Ka Sani Game Da Sabon Mataimakin Gwamnan Jihar Zamfara

Da yake karantar wasikar da Sanatan ya aike wa majalisa a zamanta na yau, shugaban majalisar dattawa, Sanata Ahmad Lawan, ya sanar da murabus ɗin Nasiha.

Lawan ya sanar da cewa Nasiha ya aje kujerarsa ta majalisar ne domin ya zama mataimakin gwamnan Zamfara.

Idan baku mance ba, gwamnan jihar Zamfara, Muhammad Bello Matawalle, ya fice daga jam'iyyar PDP ya koma APC mai mulki bayan dogon lokaci ana yaɗa jita-jita.

Sai dai matakin komawarsa APC ya fusata wasu mambobin PDP a Zamfara, waɗan da suka garzaya Kotu neman a kwace kujerarsa daga hannunsa.

Mataimakin gwamnan jihar, Barista Mahdi Aliyu Gusau, bai bi uban gidansa zuwa jam'iyyar APC ba, hakan ya sa alaƙa ta yi tsami tsakanin mutanen biyu.

Domin nuna goyon baya ga gwamna, Majalisar dokokin jahar Zamfara ta tsige Mahdi Gusau daga kujerarsa bisa laifukan da suka ce ya aikata.

Kara karanta wannan

Karin bayani: Majalisa ta amince da kudurin takara ga 'yan takara masu zaman kansu

A wani labarin kuma Yan bindiga sun bindige Hadimin gwamna har Lahira a wurin ta'aziyya

Wani wanda ke tare da mamacin ya bayyana cewa sun baro wurin Jana'izar da suka halarta yayin da maharan suka tare su.

A halin yanzun dakarun sojoji sun bazama cikin daji domin nemo gawar mutumin, bayan sun yi gaba da ita.

Asali: Legit.ng

Online view pixel