Muhammad Hassan Nasiha: Abubuwa 5 Da Ya Kamata Ka Sani Game Da Sabon Mataimakin Gwamnan Jihar Zamfara

Muhammad Hassan Nasiha: Abubuwa 5 Da Ya Kamata Ka Sani Game Da Sabon Mataimakin Gwamnan Jihar Zamfara

Zamfara - A ranar Laraba, 23 ga watan Fabrairun 2023, majalisar Jihar Zamfara ta tabbatar da nadin Sanata Muhammad Hassan a matsayin mataimakin gwamnan Jihar Zamfara.

Gwamnan Bello Matawalle ya nada Sanata Nasiha bayan tube Mahdi Aliyu Gusau a matsayin mataimakin gwamnan wanda ‘yan majalisar jihar suka tabbatar.

Muhammad Hassan Nasiha: Abubuwa 5 Da Ya Kamata Ka Sani Game Da Sabon Mataimakin Gwamnan Jihar Zamfara
Muhammad Hassan Nasiha: Abubuwa 5 Da Ya Kamata Ka Sani Kan Sabon Mataimakin Gwamnan Jihar Zamfara. Hoto: Abdulwali Anwar Tahir
Asali: Twitter

Akwai abubuwa muhimmai da suka dace a sani dangane da sabon mataimakin gwamnan Jihar Zamfara.

1. Tarihi da karatun sa

Shekarun Sanata Nasiha 61 da haihuwa kuma daga yankin Zamfara ta tsakiya yake. An haife shi a ranar 12 ga watan Disamban 1960 kamar yadda PM News ta bayyana.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Kara karanta wannan

Zamfara: Sabon mataimakin gwamna Matawalle ya yi murabus daga kujerar Sanata

Kuma yana da diploma a fannin jinya da anguwar zoma.

2. Yanzu haka sanata ne mai ci

Har sai da aka mayar da shi mataimakin gwamnan Jihar Zamfara, Sanata Nasiha dan majalisar dattawa ne na 9. Shi aka zaba a matsayin sanata a 2007 kuma shi ya fara wakiltar mazabar Zamfara ta tsakiya, kamar yadda Daily Trust ta bayyana.

A majalisa ta tara shi ne shugaban kwamitin yanayi na majalisar.

3. Tsohon jigo ne na jam’iyyar PDP

Sanata Nasiha mamba ne na jam’iyyar PDP har sai bayan sauya shekar gwamna Matawalle inda suka koma jam’iyyar APC.

An tsige Mahdi Aliyu Gusau a matsayin mataimakin gwamna bayan ya ki bin Matawalle da sauran ‘yan jam’iyyar PDP da suka koma APC.

4. Nasiha ya taba fadi takarar sanata a shekarar 2011

A zaben 2011 Sanata Kabiru Marafa ya maka Sanata Nasiha da kasa.

Bayan fadi zaben, ya daukaka kara a 2019, ya garzaya kotun koli inda ta kwace kujerar dan APC wanda ya tsaya takara akan kin yin zaben fidda gwani a jihar.

Kara karanta wannan

'Yan Bindiga Sun Sake Yin Garkuwa Da Sarki a Jihar Arewa

5. Kujerun siyasar da ya rike

Sanata Nasiha ya rike kujeru da dama na siyasa wadanda aka nada shi. Ya taba rike kujerar kwamishinan lafiya, kwamishinan hada-hadar kasuwanci, na gidaje da kuma na harkokin kananun hukumomi a tsakanin 1999 da 2007.

Asali: Legit.ng

Online view pixel