Evans: Ko Kaɗan Bai Nuna Alamar Nadama Ba Yayin Shari’arsa Na Shekaru Hudu, Alƙali

Evans: Ko Kaɗan Bai Nuna Alamar Nadama Ba Yayin Shari’arsa Na Shekaru Hudu, Alƙali

  • Kotu ta yanke wa wani mai garkuwa da mutane, Chukwudimeme Onwuamadike wanda aka fi sani da Evans, hukuncin daurin rai da rai akan hada kai da wasu mutane biyu wurin garkuwa da wani Mr Donatius Dunu
  • Alkali Hakeem Oshodi na babbar kotun Ikeja bayan yanke wa Evans da sauran mutane biyun hukunci ya ce duk da yadda aka gabatar da shaidu kwarara akan su basu nuna alamar danasani akan laifukan su ba
  • Rahotanni sun nuna yadda shari’ar wacce aka kwashe sa’o’i uku ana yi ta fallasa cewa duk wasu alamu da shaidu sun nuna cewa Evans da sauran mutane biyun sun hada wurin aika-aikar

Legas - Alkali ta yanke hukunci ga wani mai garkuwa da mutane, Chukwudimeme Onwuamadike wanda aka fi sani da Evans, da sauran mutane biyu da aka kama da laifin garkuwa da Mr Donatius Dunu, shugaban Maydon Pharmaceuticals Ltd.

Kara karanta wannan

Bayan watanni 6, an gurfanar da wadanda ake zargi da hallaka yaron Sanata a gaban kotu

Alkalin babbar kotun Ikeja, Justice Hakeem Oshodi, ya yanke wa Evans da sauran mutane biyu hukuncin daurin rai da rai, inda yace basu nuna alamar nadana ba akan aika-aikar da suka yi duk da shaidun da aka gabatar akan su.

Ko Kaɗan Evans Bai Nuna Alamar Nadama Ba Yayin Shari’arsa Na Shekaru Hudu, Alƙali
Alƙali: Ko Kaɗan Evans Bai Nuna Alamar Nadama Ba Yayin Shari’arsa Na Shekaru Hudu
Asali: Twitter

Gwamnatin Jihar Legas ta gurfanar da Evans da sauran mutane 5 a gaban kotu, Vanguard ta ruwaito.

Rahotanni sun nuna yadda hukuncin wanda aka kwashe sa’o’i uku ana yi ya bayyana cewa tabbas Evans da sauran mutane biyun, Uche Amadi da Okwuchukwu Nwachukwu sun yi aika-aikar.

Alkalin ya kama su dumu-dumu da aikata laifukan

Alkalin ya yanke musu hukunci bayan kama su sa laifukan makirci da kuma garkuwa da mutane.

Sai dai ya wanke Ogeshi Uchechukwu, Chilaka Ifeanyi wanda tsohon soja ne tare da sallamar wani Victor Aduba, wanda shima tsohon soja ne.

Kara karanta wannan

El-Rufai kan batun rashin tsaro: Halin da muke ciki a Arewa maso yamma ya fi na Boko Haram muni

Vanguard ta nuna yadda Oshodi ya ce basu da wani alaka da ta hada su da laifukan.

A cewarsa:

“A bayyane yake cewa duk wadannan mutane ukun basu nuna sun yi danasani akan laifukan da suka yi. Duk da tarin hujjojin da aka gabatar akan su, kuma sun yi kokarin wanke kansu.
“Kotu ta kula da yadda masu garkuwa da mutanen suka nuna kwarewarsu kuma sun azabtar da wanda suka kama har lokacin da ya bar hannun su. Wajibi ne a koya musu darasi. Don haka dole a yanke musu hukuncin da ya yi daidai da su.
“Sashi na 2(1) na dokar hani akan garkuwa da mutane na Jihar Legas, 2017 ta sanya daurin rai da rai a matsayin hukuncin mai garkuwa da mutane. Don haka kotu baza ta daga kafa ba.”

Ya ci gaba da cewa:

“Hakan yasa kotu ta yanke wa mai laifi na daya, biyu da na hudu, Chukwudimeme Onwuamadike wanda aka fi sani da Evans, Uche Amadi da Okwuchukwu Nwachukwu, ko wannen su hukuncin daurin rai da rai. Wannan shi ne hukunci da kotu ta yanke.”

Kara karanta wannan

Ana Shirin Biki, An sace Amarya da wasu mutum 5 a cikin garin Kaduna

Tun asali Evan ya ce azabar da ‘yan sanda suka yi masa ne ya sanya ya dinga murmushi yayin amsa laifinsa

Da farko Oshodi ya yi fatali da korafin da Evans ya yi akan illar da ‘yan sanda suka yi masa kamar yadda ya bayyana, wanda hakan ya ci karo da sashi na 9(3) na Administration Criminal Justice.

Alkalin ya ce bidiyoyi biyu na Evans wanda aka nuna wa kotu sun bayyana shi yana murmushi yayin da yake bayyana laifukansa.

Ya kara da cewa idan mutum ya yi dubi da bidiyon zai gane cewa babu wata alamar azaba a jikin sa.

Oshodi ya nuna inda Evans ya yi ikirarin cewa yana gida tare da matarsa a ranar 14 ga watan Fabrairu da aka yi garkuwa da Dunu.

Lauyan Evans ya nema masa rangwame daga kotu

Kafin a yanke hukuncin, lauyan Evans, Mr. H. O. Ajibola ya bukaci kotu ta rangwanta masa, ta yarda da cewa wannan ne karon Evans na farko.

Kara karanta wannan

Wadanda Suka Sace Dagaci Da Mutum 14 Sun Rage Kudin Fansa, Yanzu Sun Ce a Basu Buhun Shinkafa 2 Da N4m

Lauyan Olanrewaju Ajanaku, Nwachukwu ya bukaci kotu ta yi sassauci ga wanda yake karewa, inda yace mutumin mai yara uku ya yi nadama.

Sakatariyar ma’aikatar shari’a ta Jihar Legas, Ms Titilayo Shitta-Bey, a bangarenta ta bukaci kotu ta yanke musu hukunci mai tsanani don hakan ya zama izina akan su.

Asali: Legit.ng

Online view pixel