Yan bindiga sun yi garkuwa da Amarya ana gab da aurenta da wasu mutum 5 a Kaduna

Yan bindiga sun yi garkuwa da Amarya ana gab da aurenta da wasu mutum 5 a Kaduna

  • Wata budurwa mai suna Khadija da ake gab da ɗaura aurenta ta shiga hannun yan bindiga a Rigachikum dake cikin Kaduna
  • Wata mata da 'ya'yanta ke cikin waɗan da aka sace, ta ce suna cikin bacci maharan suka shigo, suka tafi da Kadija, waya da Burodi
  • Yan ta'addan sun kuma tasa wasu mutum biyar, harin dai shi ne karo na farko da aka kai yankin inji wani shugaban al'umma

Kaduna - Yan bindiga sun farmaki Anguwar Rigachikun, dake karamar hukumar Igabi, cikin garin Kaduna, sun sace wata budurwa dake shirin zama amarya da wasu mutum 5.

Daily Trust ta tattaro cewa yan ta'addan sun kai hari yankin wanda ke kusa da Kasan Dam da misalin karfe 1:00 na daren ranar Laraba.

Maharan sun kutsa gida bayan gida suka zabi wasu mutane dake zaune a yankin, cikinsu harda Amarya mai shirin fara Amarci.

Kara karanta wannan

Yanzun Nan: Yan bindiga sun halaka babban jami'in Kwastam a garin Kaduna

An sace Amarya a Kaduna
Yan bindiga sun yi garkuwa da Amarya na gab da aurenta da wasu mutum 5 a Kaduna Hoto: punchng.com
Asali: UGC

Wata mata da ƴaƴan ta ke cikin waɗan da maharan suka sace, tace Amaryar mai suna Khadija na kwance tana bacci a gida yayin da yan bindiga suka kutsa cikin ɗakin su.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Vanguard ta rahoto Matar ta ce:

"Muna tsaka da bacci lokacin da suka shigo, suka umarci Khadija da wani Shabilu su taso su biyo su. Sun ɗauki wayar salula da wani gutsuren Burodi dake kan teburi. Abin ya samu damuwa."

Shin yan bindiga sun taba kai hari yankin?

Wani shugaban mutane, Idris Abdulrasheed, ya ce wannan shi ne karo na farko da irin haka ta faru a yankin su, kuma tuni suka kai wa yan sanda rahoton abin da ya auku.

Ya ƙara da cewa har yanzun da yake magana, yan bindigan ba su tuntuɓi iyalan mutanen da lamarin ya shafa ba.

Kara karanta wannan

Wata sabuwa: Yan bindiga sun yi garkuwa da jami’in tsaro da wasu mutane a sabon harin Kaduna

ASP Mohammed Jalige, kakakin rundunar yan sanda reshen jihar Kaduna, bai ɗaga kiran waya ko ɗaya ba a jiya Laraba domin jin ta bakin su.

A wani labarin kuma wani Matashin ɗan shaye-shaye ya yi sanadin mutuwar mahaifiyarsa saboda ta masa nasiha ya dena ɗabi'ar shan kwayoyi

Jami'an yan sanda sun yi ram da mutumin mai suna Garba Abubakar kan zargin ya shake mahaifiyarsa, Salamatu Abubakar, kuma likita ya tabbatar rai ya yi halinsa.

Lamarin ya faru a jihar Gombe, yan sandan sun kuma kama wani da ya yi lalata da yarinyar makocinsa yar shekara 10 a duniya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel