Abin Da Yasa Buhari Baya Raba Wa Mutane Kuɗi, Femi Adesina

Abin Da Yasa Buhari Baya Raba Wa Mutane Kuɗi, Femi Adesina

  • Kakakin Shugaba Muhammadu Buhari, Femi Adesina ya ce shugaban kasar bai yarda da ya rika raba wa mutane kudi ba don ai masa alfarma ko cin hanci
  • Adesina ya ce Buhari ya gwammace ya yi amfani da kudi wurin tallafawa talakawa, gajiyayyu da marasa galihu da yi musu ayyuka shi yasa suke sonsa
  • Kakakin na shugaban kasa ya ce wannan halin na tausayawa talakawa da mai gidansa ke da shi yasa duk lokacin da za a yi zabe ya ke samun miliyoyin kuri'un talakawa

Femi Adesina, mashawarci na musamman ga Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ce mai gidansa ya gwammace ya kashe kudi wurin taimakawa talakawa da marasa galihu a maimakon bada kudin domin a yi masa alfarma.

Adesina ya bayyana hakan ne cikin wani rubutu da ya wallafa a shafinsa na Facebook a ranar Alhamis mai lakabin, ‘Buhari’s Kind of Kindness’.

Kara karanta wannan

Buhari: Ba Zan Zarce 2023 Ba, Na Yi Rantsuwa Da Kur'ani

Abin Da Yasa Buhari Baya Ba Wa Mutane Kuɗi, Femi Adesina
Femi Adesina: Abin Da Yasa Buhari Baya Ba Wa Mutane Kuɗi. Hoto: Fadar Shugaban Kasa

Mai magana da yawun shugaban kasar ya ce jajircewa wurin hidimtawa talakawa da kaunar da ya ke yi wa marasa galihu ya sa ya yi nasara a zaben 2015 ya kuma zarce a 2019.

Ya ce a maimakon bada toshiyar baki ko cin hanci, Buhari ya gwammace ya yi amfani da kudin domin tallafawa mutane mabukata a sassan kasar nan.

"Buhari ba zai baka buhun kudi ba domin ka masa alfarma ba. A maimakon hakan, zai bada kudin ne domin yin ayyukan alheri, jin kan marasa galihu da talakawa da mabukata," ya rubuta.

Hakazalika, Adesina ya bayyana maigidansa a matsayin 'mutum mai tausayin talakawa, gajiyayyu da marasa galihu.'

Wani sashi na rubutun ya ce, "Yana kaunar su sosai, kuma suma suna sonsa sosai. Wannan shine Shugaba Muhammadu Buhari.

Kara karanta wannan

Wani bawan Allah ya halaka babban abokinsa kan Lemun kwalba na N150

"A kan ce mutumin yana da kuri'u a kalla miliyan 12 suna jiransa a sassa daban-daban na kasar tun kafin a fara kada kuri'a a babban zabe.
"Talakawa da marasa galihu sune suka fi yawa cikin masu kada kuri'a. Suna taruwa a wurinsa kamar yadda zuma ke taruwa a gidansu."

Adesina ya kuma ce irin wannan tausayin ta talakawa ne yasa Buhari ya kafa Ma'aikatar Jin Kai, ya kuma nada Sadiya Umar Farouq a matsayin jagora.

Domin a cigaba da taimakawa talakawa, hakan yasa talakawa ke son Buhari domin ya damu da matsalolinsu kuma a kullum yana tunanin yadda zai tallafa musu.

Buhari: Na Ji Daɗin Yadda Masu Hannu Da Shuni Suka Gane Cewa Canja Najeriya Ba Aikin Mutum Ɗaya Bane

A wani labarin, Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ce ya yi farin cikin sanin cewa kusoshin Najeriya sun gane cewa canja kasar nan aikin kowa ne, The Cable ta ruwaito.

Kara karanta wannan

2023: El-Rufai ya magantu kan kudirin takarar shugaban kasa, ya bayyana wanda zai marawa baya

Kamar yadda kakakin shugaban kasa, Femi Adesina ya bayyana a wata takarda, Buhari ya yi wannan furucin ne a ranar Lahadi a wata liyafa ta girmama shugabannin kwamitin kasuwanci, siyasa, kafafen watsa labarai da sauran ma’aikata.

Dama a watan Janairun 2021 The Cable ta bayyana yadda Buhari ya zargi masu fada a jin kasar nan da kawo cikas ga gwamnatin sa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel