Wani mutumi ya halaka babban abokinsa kan Lemun kwalba na N150

Wani mutumi ya halaka babban abokinsa kan Lemun kwalba na N150

  • Wani mutumi ya yi ajalin babban abokinsa da suka haɗu a wurin mai POS kan lemun kwalba na Naira N150
  • Hukumar yan sanda ta jihar Ekiti ta maka shi a gaban Kotun Majistire, kuma tuni alalkali ya aika da shi magarƙama
  • Mutumin ya ce ya siya lemun Chapman abokinsa ya kwace, hakan ya bata masa rai, ya fasa kwalba ya jefe shi da ita

Ekiti - Kotun Majistire ta garƙame wani mutumi ɗan kimanin shekara 42, Oluwafemi Olaifa, a gidan gyaran hali dake Ado-Eikiti, jihar Ekiti, bisa zargin kashe abokinsa.

Daily Trust ta rahoto cewa mai gabatar da kara, Insufekta Olubu Apata, ya shaida wa kotu cewa mutumin ya aikata laifin da ake tuhumarsa ranar 20 ga watan Fabrairu.

Insufekta Apata na hukumar yan sanda ta jihar Ekiti ya faɗa wa Alkali cewa wanda ake zargi ya halaka wani mutumi mai suna, Ayoola Ajayi.

Kara karanta wannan

Matashi ya shake mahaifiyarsa har Allah ya mata rasuwa saboda ta masa Nasiha a Gombe

Taswirar jihar Eikiti
Wani mutumi ya halaka babban abokinsa kan Lemun kwalba na N150 Hoto: channelstv.com
Asali: UGC

Apata yace a jawabin da Mutumin ya yi wa yan sanda, ya nuna cewa mamacin babban abokinsa ne kuma amininsa, kuma a ranar sun haɗu a wurin mai POS dukansu sun je cire kudi.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Meyasa ya halaka abokin nasa?

Insufekta Apata ya ce:

"Wanda muke kara yace ya siya Lemun Kwalba na Chapman kan N150, ba zato sai Ajayi ya kwace daga hannunsa ya shanye lemun tun kafin ya biya kuɗin."
"Hakan ya tunzura shi kuma yayin haka ne ya fasa kwalbar Barasa a shagon ya jefe shi da ita."
"Ya ƙara da cewa fasassar kwalbar ta same shi a wuya kuma ta yanke shi, wanda hakan ya yi sanadin mutuwarsa a Asibiti."

Mai gabatar da ƙaran ya roki Mai Shari'a ya bada umarnin tsare wanda ake zargin kafin jin matakin da ofishin Daraktan DPP zai ɗauka.

Kara karanta wannan

Abu ya girma: An bayyana babban abin da zai tarwatsa jam'iyyar APC nan gaba kadan

Wane hukunci alƙali ya yanke?

Alkalin Kotun, Mai Shari'a Kehinde Awosika, ta karɓi bukatar mai gabatar da ƙara, inda ta umarci a tsare mutumin a gidan gyaran hali.

Bayan haka kuma sai ta sanar da ɗage sauraron ƙarar har zuwa ranar 28 ga wata mai kamawa, Maris, 2022.

A wani labarin kuma Gwamnan Kaduna yace kamata ya yi a baiwa mazauna Legas damar shiga Aljanna kyauta saboda wahalar Cunkoso

Gwamna Nasiru El-Rufa'i na jihar Kaduna ya ce wahalar da mutanen Legas ke sha wajen cunkoson ababen hawa na ba shi mamaki.

Gwamnan yace mutanen da suka rayu har tsawon shekar 20 a irin wannan yanayin lallai sun cancanci shiga Aljanna kyauta.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel