Sojoji sun hallaka yan bindiga 55 kusa da makarantar Soji NDA

Sojoji sun hallaka yan bindiga 55 kusa da makarantar Soji NDA

  • Jami'an Sojin Najeriya sun samu nasarar hallaka tsagerun yan bindiga 55 a jihar Kaduna
  • Mai magana da yawun hedkwatar tsaron Najeriya ya bayyana cewa anan hari ya auku kusa da jami'ar horon Sojojin Najeriya
  • Wannan shine karo na biyu da za'a yi artabu tsakanin Soji da yan bindiga kusa da makarantarsu

Abuja - An yi musayar wuta tsakanin dakarun Sojin Operation Thunder Strike/Whirl Punch da tsagerun yan bindiga a yankin Labi, hanyar Kaduna zuwa Birnin Gwari.

Akalla yan bindiga 55 suka bakunci lahira cikin kimanin su 75 da aka tirke kusa da makarantar Sojojin Najeriya NDA a Kaduna.

Diraktan yada labarai na hedkwatar tsaro, Manjo Janar Benard Onyeuko, ya bayyana hakan ranar Alhamis yayin hira da manema labarai, rahoton DailyTrust.

Makarantar Soji NDA
Sojojin sun hallaka yan bindiga 55 kusa da makarantar Soji NDA Hoto: NDA
Asali: UGC

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Onyeuko ya yi bayanin cewa yan bindigan sun sha ruwan wuta daga sama da kuma harsasan sojin kasa.

Yace:

"Jami'an Sojin sama sun kai hari mabuyar yan bindga a kudancin Damari dake karamar hukumar Birnin Gwari ta jihar Kaduna bayan binciken kwakwaf."
"Harin Sojin saman ya hallaka yan bindiga kusa da NDA, kuma sakamakon haka yan bindiga 55 sun mutu."

Sojojin sun hallaka yan bindiga 20 da suka yi kokarin sake kai harin makarantar Soji NDA

Haka Rundunar Sojin Operation Thunder Strike kwanakin baya sun hallaka akalla yan bindiga 20 da suke kokarin kai harin makarantar horar Sojojin Najeriya watau NDA dake jihar Kaduna.

Wani rahoton PR Nigeria ya bayyana cewa yan bindigan, kimanin su 50 kan babura sun durfafi makarantar da yammacin Alhamis 10 ga Febrairu, suna kokarin shiga.

Sojojin sun samu nasarar kawar da yan ta'addan ne sakamkon bayanan da suke samu cewa an ga yan bindiga suna rastawa cikin daji.

Asali: Legit.ng

Online view pixel