Karin bayani: Sojin Najeriya sun ragargaji 'yan ISWAP da Boko Haram a Adamawa

Karin bayani: Sojin Najeriya sun ragargaji 'yan ISWAP da Boko Haram a Adamawa

  • Rundunar sojojin Najeriya tare da hadin gwiwar rundunar 'yan sa kai ta farar hula sun kai farmaki kan 'yan ta'adda
  • A wani rahoto da rundunar sojin ta fitar, an samu nasarar fatattakar mayakan Boko Haram da ISWAP da dama; aikin da sojojin bataliya ta 144 dake Madagali-Adamawa suka yi
  • A halin da ake ciki, Hedkwatar Sojojin Najeriya, a sakon da ta wallafa a shafin Twitter ta bayyana cewa an kwato makamai da alburusai da dama daga farmakin da sojojin suka kai

Mandara, jihar Adamawa - Rundunar sojin Najeriya ta bayyana cewa, ta ragargaji wasu 'yan ta'addan Boko Haram/ISWAP da ke kokarin janyewa juna bayan ba hammata iska a wani yankin jihar Adamawa.

Rundunar sojin ta ce ta samu rakiyar 'yan sa kai na Civilian JTF, inda ta samu bayanai na sirri kan motsin 'yan ta'addan da ya kai ga nasarar hallaka wasu a yau Litinin 21 ga watan Fabrairu.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Mayaƙan ISWAP sun mamaye sansanin Sojoji a Borno, sun yi mummunar barna

Rundunar soji ta hallaka 'yan ta'addan Boko Haram da ISWAP
Da dumi-dumi: Sojojin Najeriya sun ragargaji kasurguman 'yan Boko Haram/ISWAP a Adamawa | Hoto: @HQNigerianArmy
Asali: Twitter

Rundunar ta bayyana cewa, lamarin ya faru ne jim kadan bayan da 'yan ta'addan suka ba hammata iska, inda suke kokarin janyewa juna bayan fafatawarsu.

Hoton da sanarwar ke dauke dashi ya nuna alamar an kwato makamai da wasu kayayyaki daga hannun 'yan ta'addan.

A shafinta na Twitter, rundunar sojin Najeriya fitar da sanar, ta ce:

"Ta amfani da rahoton sirri, a yau sojojin bataliya ta 144 Madagali-Adamawa tare da hadin gwiwar Civilian JTF sun yi kwanton bauna kan 'yan ta'addan ISWAP/BHT da ke janyewa bayan wata arangama tsakanin kungiyoyin ta’addancin. An kashe 'yan ta'adda da dama a tsaunin Mandara."

Mayakan ISWAP sun mamaye sansanin sojojin Najeriya a jihar Borno

Sai dai, a wani labari mara dadi, kungiyar ta'addanci da ta balle daga kungiyar Boko Haram, ISWAP ta mamaye sasanin sojojin Najeriya dake Gamboru-Ngala a jihar Borno, ranar Lahadi da daddare.

Kara karanta wannan

Kun mayar da lakcarori bayi: ASUU ta caccaki gwamnatin Buhari kan batun albashi

Yan ta'addan sun farmaki sasanin sojin ne a makarantar Firamare dake garin Gamboru kuma suka tarwatsa dakarun soji, kamar yadda Leadership ta ruwaito.

Haka nan yan ta'addan sun kone sansanin baki daya a harin na ɗaukar fansa biyo bayan luguden wutan da sojoji suka musu a Tafkin Chadi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel