Sojojin sun hallaka yan bindiga 20 da suka yi kokarin sake kai harin makarantar Soji NDA

Sojojin sun hallaka yan bindiga 20 da suka yi kokarin sake kai harin makarantar Soji NDA

Kaduna - Rundunar Sojin Operation Thunder Strike sun hallaka akalla yan bindiga 20 da suke kokarin kai harin makarantar horar Sojojin Najeriya watau NDA dake jihar Kaduna.

Wani rahoton PR Nigeria ya bayyana cewa yan bindigan, kimanin su 50 kan babura sun durfafi makarantar da yammacin Alhamis, suna kokarin shiga.

Sojojin sun samu nasarar kawar da yan ta'addan ne sakamkon bayanan da suke samu cewa an ga yan bindiga suna rastawa cikin daji.

Rahoton yace kai tsaye aka tura jiragen Sojin sama don ragargazan yan bindigan.

Makarantar Soji NDA
Sojojin sun hallaka yan bindiga 20 da suka yi kokarin sake kai harin makarantar Soji NDA Hoto: NDA
Asali: UGC

An tattaro cewa sun taso ne daga kauyen Damari, dake karamar hukumar Birnin Gwari ta jihar.

An gansu cikin ruga da babura kimanin 50.

Wani a gidan Soja ya bayyanawa cewa:

"Yayinda suka ga jiragen, sai su yan bindiga suka fara boyewa cikin dajin. Hakan ya sa Sojoji sukayi musu ruwan wuta inda aka ga wasu suna guduwa."
"Kuma kamar yadda aka saba, bayanan da aka samu ranar Juma'a bayan hari daga bakin Sojoji da mutan gari sun nuna cewa an hallaka kimanin mutum 20 cikin yan bindigan."
"Hakazalika an dakile yunkurin kunyata makarantar Soji da Gwamnatin nan."

Asali: Legit.ng

Online view pixel