Duk wanda yayi mana shisshigi kan yakinmu da Ukraniya zai fuskanci ukuba, Shugaban kasan Rasha

Duk wanda yayi mana shisshigi kan yakinmu da Ukraniya zai fuskanci ukuba, Shugaban kasan Rasha

  • Shugaban kasar Rasha ya gargadi Amurka, Ingila, Faransa, Jamus da sauran kasashen duniya su kama kansu kan rigimarsa da Ukraine
  • Rasha a ranar Alhamis ta fara kai hare-hare birnin Kyiv kuma mutane sun fara guduwa daga garin
  • Ministan harkokin wajen Ukraniya ya yi kira ga kasashen duniya su kawo mata dauki

Shugaban kasar Rasha, Vladimir Putin, ya gargadi Amurka da sauran kasashen Turai su yi hattara kada su sa baki kan yakinsu da Ukraniya ko kuma su fuskanci mumunar ukuba.

Putin ya bayyana hakan ne da safiyar Alhamis yayinda yayi jawabi ga al'ummar kasar kan yanke shawarar kai hari Ukraniya.

Yace:

"Shirye muke da duk sakamakon da zai biyo baya. Duk wanda yayi kokarin hana mu ko yayi mana barazana, al'ummarmu su sani cewa zasu mayar da martanin da ba'a taba gani ba.

"Hakkinmu ne kare mutanen da gwamnatin Ukraine ta kwashe shekaru takwas tana zalunta."

Shugaban kasan Rasha
Duk wanda yayi mana shisshigi kan yakinmu da Ukraniya zai fuskanci ukuba, Shugaban kasan Rasha Hoto: Kremlin
Asali: Getty Images

Rasha ta fara kai harin bama-bamai

Dakarun Sojin kasar Rasha sun harba makami mai linzami cikin biranen Ukraniya yayinda Sojin kasa suke kokarin shiga, jami'an gwamnati da manema labarai sun bayyana.

Wannan ya biyo bayan sanarwar da Shugaban kasar Rasha, Vlamidir Putin, yayi cewa zasu fara kai hari gabashin Ukraniya.

Yan mintuna bayan sanarwar Putin a tashar Talabijin na kasar aka fara jin karar bama-bamai cikin birnin tarayyar Ukraniya, Kyiv.

Ministan harkokin wajen Ukraniya, Dmytro Kuleba, a jawabin da ya saki a shafinsa na Tuwita ya bayyana.

Asali: Legit.ng

Online view pixel