Nan babu dadewa zan zama tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari

Nan babu dadewa zan zama tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari

  • Shugaba Buhari ya sanar da cewa kwanaki kadan suka rage ya zama tsohon shugaban kasar Najeriya
  • Buhari ya yi kira ga shugabanni da kada su tozarta rantsuwar da suka yi da littafan addini da kuma yardar da mutane suka basu
  • Shugaban kasar ya sanar da cewa wa'adin mulkinsa na cika zai tattara komatsansa ya bar kujerar kamar yadda kundun tsarin mulki ya tanadar

Lafia, Nasarawa - Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya sanar da cewa kwanakinsa a matsayin shugaban kasar Najeriya kayyadaddu ne kuma komai jimawa ko dadewa zai zama tsohon shugaban kasa.

A saboda hakan ne shugaban kasan ya shawarci shugabanni da suka yi rantsuwa da littafan addini da ya zama dole kada su ci zarafin wannan yardar da aka basu ta shugabanci, Vanguard ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Duk shugaban da ya rantse da AlQur'ani kada ya kuskurar yaci amana, Shugaba Buhari

Nan babu dadewa zan zama tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari
Nan babu dadewa zan zama tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari. Hoto daga @BashirAhmaad
Asali: Twitter

A yayin jawabi a fadar sarkin Lafia, Alkali Sidi Bage Muhammad 1 mai ritaya, shugaban kasa Muhammadu Buhari yayin ziyarar aiki da ya kai jihar Nasarawa ya jaddada cewa bashi da niyyar cigaba da zama a mulki fiye da tanadin kundin tsarin mulki.

Kamar yadda yace, "Sarautar gargajiya ita har karshen rayuwa ce. Amma a kundun tsarin mulki, mu ba hakan bane. Ba zan iya wuce wa'adin mulki biyu ba kuma na dauka rantsuwa da Qur'ani cewa zan kiyaye kundin tsarin mulkin Najeriya.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

”A bar siyasa a gefe, duk abinda aka ce an yi rantsuwa da Qur'ani, dole ne mu kiyaye. Dole ne mu tabbatar da cewa ba za mu iya cin amanar da Allah ya bamu ba a matsayinmu na shugabanni.
"Ban taba ganin tsohon gwamna a nan ba, nima tafiya zan yi wata rana," yace.

Kara karanta wannan

Shin za ka tsaya takara a 2023: Jonathan ya ba da amsar da ba a yi tsammani ba

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya mika godiyarsa ga jama'ar jihar Nasarawa kan tarbar da suka yi masa inda ya bayyana farin cikinsa kan kyan da ya ga jihar ta yi tun bayan ziyarar da ya kai 2019, Vanguard ta ruwaito.

Buhari ya tafi Nasarawa, Osinbajo ya dura birnin Maiduguri domin wata ziyara

A wani labari na daban, a yau Alhamis ne mataimakin shugaban kasa, Yemi Osinbajo ya dura birnin Maiduguri, jihar Borno a wata ziyarar rana daya da ya kai.

A cewar TVC, Osinbajo ya samu tarbar gwamnan jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum yayin da ya sauka a jihar.

Ziyarar Osinbajo dai na zuwa ne jim kadan bayan da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya sauka a jihar Nasarawa a wata ziyarar aiki ta kwanaki biyu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel