Yanzu-Yanzu: Shugaba Buhari Ya Dira Lafia, Babban Birnin Jihar Nasarawa

Yanzu-Yanzu: Shugaba Buhari Ya Dira Lafia, Babban Birnin Jihar Nasarawa

Lafia - Shugaba Muhammadu Buhari ya isa garin Lafia, babban birnin Jihar Nasarawa domin ziyarar aiki na kwanaki biyu, rahoton Vanguard.

Shugaban kasar, wanda ya zo a cikin helicofta 5N-FG2, ya dira a filin tashi da saukan jirage na Lafia, misalin karfe 10 na safe.

Yanzu-Yanzu: Shugaba Buhari Ya Dira Lafia, Babban Birnin Jihar Nasarawa
Yanzu-Yanzu: Shugaba Buhari Ya Kawo Ziyara Jihar Nasarawa. Hoto: Vanguard
Asali: Twitter

Wadanda suka tarbe shi sun hada da gwamna mai masaukin baki, Abdullahi Sule, sai gwamnan Jihar Kogi, Yahaya Bello, gwamnan Jihar Kebbi, Atiku Bagudu da mataimakin gwamnan Benue da wasu manyan.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Wasu daga cikin ayyukan da Buhari zai kaddamar sun hada da sabuwar ginin Babban Bankin Kasa, CBN da karamar tashar rarraba wutar lantarki.

Saurari karin bayani ...

Kara karanta wannan

Buhari ya tafi Nasarawa, Osinbajo ya dura birnin Maiduguri domin wata ziyara

Asali: Legit.ng

Online view pixel