Felicia Adebola, Marubuciyar da Ta Rubuta Taken Alkawarin Najeriya ta Mutu

Felicia Adebola, Marubuciyar da Ta Rubuta Taken Alkawarin Najeriya ta Mutu

- Marubuciyar taken alkawarin Najeriya ta mutu a ranar Asabar da gabata bayan gajeriyar jinya

- Ta kasance malama a jami'ar Legas, ta kuma yi rubutun taken a shekarar 1976 bisa rokon 'ya'yanta

- Obasanjo ne ya gyara taken, ya kuma tabbatar da kaddamar da taken a makarantu a fadin Najeriya

Farfesa Felicia Adebola Adedoyin, marubuciyar taken alkawarin kasa na Najeriya, ta mutu a ranar Asabar bayan gajeriyar rashin lafiya.

Marigayiya Adedoyin wanda aka haifa a ranar 6 ga Nuwamba 1938 itace ta biyu cikin yara shida kuma Gimbiya daga Gidan Iji Ruling na Saki dake karamar hukumar Saki ta Yamma, yankin Oke Ogun na jihar Oyo.

Masaniyar a fannin ilimi, ta samu digirinta na uku a shekarar 1981 daga Jami’ar Legas, Nairaland ta rahoto.

Farfesa Adedoyin, wacce ta karantar a Jami'ar Legas, ta kuma kasance mai ba da shawara ga Majalisar Dinkin Duniya, ita ta rubuta taken alkawarin kasa a shekarar 1976.

KU KARANTA: Da Dumi-Dumi: Ba Mu Muka Kwamushe Fasto Mbaka Ba, inji DSS

Felicia Adebola, Marubuciyar da Ta Rubuta Taken Alkawarin Najeriya ta Mutu
Felicia Adebola, Marubuciyar da Ta Rubuta Taken Alkawarin Najeriya ta Mutu Hoto: theeagleonline.com.ng
Asali: UGC

Ta rubuta taken alkawarin ne biyo bayan damunta da 'ya'yanta suka yi wadanda ke karanta rantsuwar aminci lokacin da suke makaranta a New York, da kuma Alkawarin Jiha a Makarantar Achimota dake Ghana.

Farfesa Adedoyin ta rubuta taken ne a cikin jaridar Daily Times a ranar 15 ga Yulin 1976, a cikin wata kasida mai taken 'Aminci ga Kasa, Alkawari' da aka nuna wa Shugaban kasa na wancan lokacin, Janar Olusegun Obasanjo.

Obasanjo ya gyara taken ya kuma gabatar da shi ga Kasa a lokacin da aka kaddamar da shirin bayar da Ilimin Firamare na Bai-daya (UPE) tare da yanke hukuncin cewa duk yaran makaranta su karanta taken alkawarin kasar a taron makaranta.

A shekarar 2005, an baiwa Farfesa Adedoyin lambar yabo ta kasa, 'Officer of the Order of the Niger (OON).'. Tana karkashin kulawar yaranta, zagaye da masoyanta lokacin da ta rasu.

KU KARANTA: Gwamnatin Buhari Ta Taya Iyayen Daliban Jami'an Greenfield Jimamin Sace Yaransu

A wani labarin, Wata tankar dakon mai dauke da kayan da ake zargin man fetur ne, ta yi hatsari a kan babbar hanyar Mararaba zuwa Abuja da safiyar Talata.

An gano cewa man ya zube daga tankar da ta yi hatsari, yana kwarara ba kakkautawa zuwa shagunan da ke kusa da wuraren mazauna yankin.

Wannan ya jefa mazauna cikin rudani yayin da suka runtuma don kare lafiyarsu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel