Biki bidiri: Gwamnati ta aurar da tubabbun yan gidan magajiya a Bauchi

Biki bidiri: Gwamnati ta aurar da tubabbun yan gidan magajiya a Bauchi

  • Hukumar Hisbah reshen jihar Bauchi ta kulla aure tsakanin wasu yan gidan magajiya biyu da suka tuba
  • Daurin auren ya samu halartan manyan jami'an gwamnati ciki harda kakakin majalisar dokokin jihar Bauchi, Danlami Kawule da kwamishinan harkokin addini, Umar Kesa
  • Danlami ne ya biyawa angon ,mai suna Aliyu Usman sadaki N50,000

Bauchi - Hukumar Hisbah ta jihar Bauchi ta aurar da wasu tubabbun yan gidan magajiya guda biyu a ranar Litinin, 21 ga watan Fabrairu.

Jaridar Punch ta rahoto cewa an daura auren ne a daya daga cikin gidajen magajiya da ke Bayangari a cikin garin Bauchi.

Biki bidiri: : Hukumar Hisbah ta aurar da tubabbun yan gidan magajiya biyu a Bauchi
Biki bidiri: : Hukumar Hisbah ta aurar da tubabbun yan gidan magajiya biyu a Bauchi Hoto: @MobilePunch
Asali: Twitter

Daurin auren ya samu halartan mataimakin kakakin majalisar dokokin jihar Bauchi, Danlami Kawule; kwamishinan harkokin addini, Umar Kesa; manyan jami’an gwamnati, manyan jami’an hukumar shari’a da kuma daruruwan yan gidan magajiya.

Kara karanta wannan

Kwankwaso, ministoci da wasu manyan masu ruwa da tsaki sun yiwa Kano tsinke yayin da AGF Idris ya aurar da diyarsa

Punch ta kuma rahoto cewa Danlami Kawule ne ya biyawa ango, Aliyu Usman sadakin N50,000.

Kwamishinan harkokin addini ya bayar da umurnin daura auren bayan ya saurari bayanai daga wakilin ango.

Shugaban hukumar shari'a ta jihar Bauchi, Sheik Mustapha Baban – Illela, wanda ya daura auren, ya bayyana cewa an kulla shi ne da yardar iyayen amaryar, Sadiya Ibrahim.

Ya bayyana cewa bisa ga binciken lafiya da aka gudanar, ma'auratan na da cikakken lafiya kuma suna da ikon zama mata da miji.

Yayin da yake mika godiya a madadub shi da amaryarsa, Usman ya ce:

"Da izinin Allah daga yau mun tuba daga abun da muke aikatawa a baya kuma za mu chanja hali zuwa nagari."

Abuja: Jami'an tsaro sun cafke 'yan mata 27 yayin samame da suka kai gidan magajiya

Kara karanta wannan

Mu ma nan ba da dadewa ba da yiwuwan mu shiga yajin aiki, Kungiyar Malaman Poly ASUP

A wani labari na daban, mun ji cewa ma’aikatan ofishin samar da walwalan babban birnin tarayya, Abuja, tare da taimakon jami’an tsaro sun kai samame wani fitaccen gidan karuwai a Abuja, SaharaReporters ta ruwaito.

Sun kama a kalla karuwai 27, a cewar mukaddashin darektan samar da walwalar na FCT Abuja, Sani Amar wanda ya jagoranci samamen a ranar Juma’a.

Bisa ruwayar SaharaReporters, Amar ya ce ministan Abuja, Dr Ramatu Aliyu ta yi kira akan yaki da duk wasu masu harkoki a gidan karuwai da karuwan a cikin babban birnin.

Asali: Legit.ng

Online view pixel