Tashin hankali: 'Yan bindiga sun farmaki tawagar kwamishina, ya sha sudin goshi

Tashin hankali: 'Yan bindiga sun farmaki tawagar kwamishina, ya sha sudin goshi

  • Wasu ‘yan bindiga sun sake kai wani mummunan hari a Enugu, yayin da suka farmaki kwamishinan filaye na jihar
  • Wannan harin ya yi sanadin mutuwar jami’an tsaronsa guda biyu yayin da suke artabu da ‘yan bindigar
  • Lamarin da ya faru a ranar Lahadi, 20 ga watan Fabrairu, rundunar ‘yan sandan jihar Anambra ta tabbatar da faruwar lamarin

Jihar Enugu - A ranar Litinin, 21 ga watan Fabrairu, an shiga tashin hankali a Enugu bayan da aka samu labarin cewa, kwamishinan filaye na jihar, Mista Chidi Aroh, ya tsallake rijiya da baya bayan da wasu ‘yan bindiga suka kai masa hari.

Biyu daga cikin jami’an tsaronsa, wadanda suka yi artabu da ‘yan bindigar, ana fargabar sun mutu, saboda har yanzu ba a gano gawarwakinsu ba.

Kara karanta wannan

Lai Mohammed: Lakani 1 da Gwamnati ta yi amfani da shi aka samu saukin ‘yan bindiga

Kwamishina ya tsallake rijiya da baya
Tashin hankali: 'Yan bindiga sun farmaki tawagar kwamishina, ya sha sudin goshi | Hoto: Enugu Metropolitan Network
Asali: UGC

Jaridar Punch ta rawaito cewa lamarin ya faru ne a ranar Lahadi, 20 ga watan Fabrairu, yayin da Aroh ke dawowa daga Anambra, inda ya halarci wani taro.

Yadda abin ya faru

Majiyar ‘yan sandan ta ce an kashe jami'an tsaron kwamishinan biyu ne a lokacin da ‘yan bindigar suka yi wa kwamishinan kwanton bauna.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Jaridar Vanguard ta rahoto hukumar 'yan sanda na cewa:

"‘Yan bindiga sun yi wa motar su kirar Hilux kwanton bauna a wata unguwa a Anambra, suka harbe su har lahira yayin da kwamishinan ya yi sa’ar tserewa a motarsa kirar SUV.2

'Yan sanda sun tabbatar da faruwar lamarin

Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Anambra, Ikenga Tochukwu, ya tabbatar da faruwar harin, inda ya kara da cewa lamarin ya faru ne a kan hanyar Ukpo zuwa Nimo.

Kara karanta wannan

‘Yan bindiga sun ‘aure’ wasu yaran makarantar da aka gagara kubutarwa, sun yi masu ciki

A cewarsa, jami'an tsaron kwamishinan sun yi artabu da ‘yan bindigar ne a wata fafatawar da suka yi, wanda hakan ne ya kai ga kubutar kwamishinan da direban sa.

Yace:

“Rundunar, bayan samun bayanai, ta tura jami’anta zuwa yankin. Har yanzu dai ba a san inda ‘yan sandan biyu suke ba, kuma ana ci gaba da gudanar da bincike.”

Yadda dan sakai ya yi wa wani mutum fashi ya kuma halaka shi a Sokoto

A wani labarin, an kama wani dan haramtaciyyar kungiyar Yan Sakai, Sidiq Kuruwa, saboda fashi da kashe wani bafulatani mai suna Riskuwa Kalamon, a karamar hukumar Tureta a Jihar Sokoto, Daily Trust ta ruwaito.

An gano cewa Kuruwa ta ya sahun bafulatanin ne bayan ya sayar da shanunsa a Kasuwar Tsamiya a yayin da ya ke shirin aurar da yarsa.

Kuruwa, yayin da jami'an Hukumar Tsaro na NSCDC suka yi holensa ya ce ya raba kudin tare da abokinsa da yanzu ake nemansa, rahoton Daily Trust.

Kara karanta wannan

Da dumi-dumi: Harin jirgin yakin Najeriya ya kashe yara bakwai a Jamhuriyar Nijar

Asali: Legit.ng

Online view pixel