Sharri aka min, ina da ciwon sukari da hawan jini: Abba Kyari ya kai karar gwamnati kotu

Sharri aka min, ina da ciwon sukari da hawan jini: Abba Kyari ya kai karar gwamnati kotu

  • Abba Kyari, dan sandan da ke fuskantar tuhuma a gida Najeriya da waje ya kai karar gwamnatin Buhari kotu
  • Ya bayyana cewa, yana fama da rashin lafiya, kuma tun farko sharri aka yi masa, don haka yana neman beli
  • Sai dai, alkali ya yi watsi da bukatarsa, ya bayyana dalilai na kin ba da belin na Abba Kyari a yau Litinin

FCT, Abuja - DCP, Abba Kyari, wanda a halin yanzu yake hannun hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa NDLEA, bisa zarginsa da hannu a safarar miyagun kwayoyi, a ranar Litinin, ya maka gwamnatin tarayya a kotu, Vanguard ta ruwaito.

Kyari, a cikin karar da ya shigar mai lamba FHC/ABJ/CS/182/22, yana rokon kotu da ta tilasta wa hukumar NDLEA ta bayar da belinsa bisa dalilan rashin lafiya, har zuwa lokacin da za a saurari kararsa tare da yanke hukuncin neman tabbatar laifinsa.

Kara karanta wannan

An tsaurara tsaro: Majalisar jiha na shirin tsige mataimakin kakaki bisa kin jinin APC

Abba Kyari ya kai gwamnatin Buhari kotu
Wata sabuwa: DCP Abba Kyari ya maka gwamnatin Buhari a kotu saboda dalilai | Hoto: dailytrust.com
Asali: UGC

A cikin karar da ya shigar ta hannun lauyar sa, Mrs PO Ikenna, tsohon shugaban rundunar leken asiri ta IRT, ya shaida wa kotun cewa ana tsare da shi ne “saboda zargin karya da aka kakaba masa."

Duk da haka, lokacin da aka gabatar da karar, Mai shari’a Inyang Ekwo, ya lura cewa karar ta kunshi wasu abubuwan da za su bukaci martanin FG.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Kotu ta yi watsi da bukatar Abba Kyari

A rahoton Premium Times, an ce alkalin kotu ya ki amincewa da bukatar da Kyari ya nuna a gabanta saboda dalilai.

Da yake yanke hukunci kan bukatar da aka bijiro da ita, alkalin kotun, Inyang Ekwo, ya umurci wanda ya shigar da karar da ya sanar da hukumar ta NDLEA.

Alkalin kotun ya dage sauraron karar zuwa ranar 24 ga watan Fabrairu domin sauraren karar.

Kara karanta wannan

Zaben 2023: Kotu ta kori karar da ke kalubalantar cancantar Atiku na tsayawa takara

Abin da ke damun Abba Kyari

Ms Ikena ta shaida wa manema labarai jim kadan bayan dage karar cewa:

"Wanda nake karewa yana da ciwon sukari da hawan jini."

Idan baku manta ba, a ranar 14 ga watan Fabrairu ne hukumar NDLEA ta zargi Kyari na tare da wata tawagar safarar miyagun kwayoyi ta kasa da kasa.

Sanarwar da hukumar ta NDLEA ta yi ya zo ne ‘yan watanni bayan da wata kotu a Amurka ta gurfanar da shi kan wata shari’ar zamba ta intanet tare da abokin harkallarsa; Hushpuppi.

Bayan sanarwar, rundunar ‘yan sandan Najeriya ta sanar da cewa an kama Mista Kyari ne tare da wasu mutane hudu na tawagar ‘yan sandan da suke aiki tare a harkallar kwayoyi.

An gano yadda fadar shugaban kasa ta bayar da gudumawar gaggawa wurin damke Abba Kyari

A wani labarin, sabbin bayanai sun bayyana yadda aka damke fitaccen dan sanda, mataimakin kwamishinan 'yan sanda, Abba Kyari kuma aka mika shi ga hukumar yaki da fataucin miyagun kwayoyi a makon da ya gabata.

Kara karanta wannan

Zargin safara: Yadda Abba Kyari ya yi aiki da kungiyar dillalan kwayoyi a Brazil, NDLEA

Hukumar NDLEA ta bayyana cewa ta na neman Abba Kyari ido rufe, hakan ya zama dole ne bayan da hukumar 'yan sanda ta kasa ta cika umarnin NDLEA na bayar da Kyari domin amsa tuhuma, ThisDay ta ruwaito.

"Amma ganin kai tsaye fadar shugaban kasa ta shiga lamarin bayan taron manema labarai da NDLEA ta yi, hakan yasa aka gaggauta mika shi," wata majiya daga fadar shugaban kasa ta sanar. "

Asali: Legit.ng

Online view pixel