Kwankwaso, ministoci da wasu manyan kasa sun yiwa Kano tsinke yayin da AGF Idris ya aurar da diyarsa

Kwankwaso, ministoci da wasu manyan kasa sun yiwa Kano tsinke yayin da AGF Idris ya aurar da diyarsa

  • Babban akawu na tarayya, Alhaji Ahmed Idris, ya aurar da diyarsa mai suna Hafsa a jihar Kano a ranar Asabar, 19 ga watan Fabrairu
  • Manyan mutane irin su Kwankwaso, ministan tsaro, Bashir Magashi, karamin ministan kasafin kudi da tsare-tsaren kasa, Clem Agba da sauransu sun halarci daurin auren
  • An daura auren ne a masallacin Aliyu Bin Abi-Dalib kan sadaki N100,000, inda Farfesa Sambo Junaid, Walin Sokoto ya tsaya a matsayin waliyin amarya

Kano - Jihar Kano ta yi cikar kwari a ranar Asabar, 19 ga watan Fabrairu, yayin da manyan masu fada aji suka yiwa masallacin Aliyu Bin Abi-Dalib tsinke domin halartan daurin auren Hafsat, diyar babban akawu na tarayya, Alhaji Ahmed Idris.

Daga cikin manyan mutanen da suka halarci taron akwai ministan tsaro, Bashir Magashi, karamin ministan kasafin kudi da tsare-tsaren kasa, Clem Agba, da kuma shugaban hukumar kiyaye hadurra ta kasa (FRSC), Bobboyi Oyeyemi.

Kara karanta wannan

Hotunan manyan yan Kannywood yayin da suka gana da mataimakin shugaban kasa a Villa

Sauran sun hada da tsohon gwamnan jihar Kano, Rabiu Musa Kwankwaso da mataimakin gwamnan Kano, Nasiru Yusuf Gawuna, jaridar Daily Trust ta rahoto.

Kwankwaso, ministoci da sauran manyan kasa sun yiwa Kano tsinke yayin da AGF Idris ya aurar da diyarsa
Kwankwaso, ministoci da sauran manyan kasa sun yiwa Kano tsinke yayin da AGF Idris ya aurar da diyarsa Hoto: Daily Trust
Asali: UGC

Farfesa Sambo Junaid, Walin Sokoto shine ya tsaya a matsayin waliyin amarya yayin da aka biya kudin sadaki M100,000.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Da yake magana jim kadan bayan daurin auren, Idris ya yi godiya ga wadanda suka halarci taron sannan ya kyi kira ga sabbin ma’auratan da su yi rayuwa cikin kaunar juna.

Daily Trust ta nakalto AGF Idris yana cewa:

“Muna musu fatan alkhairi da addu’a kan Allah ya shige masu gaba a sabon gidansu domin daga yau sun zama iyali. Suna iya samun da ko diya ko tagwaye kwanan nan. Don haka ina masu fatan zaman lafiya kuma kada su bari a samu na uku da zai dunga sanya baki a harkokin aurensu, koda ni ne.”

Kara karanta wannan

Osinbajo ya jagoranci zaman majalisar zartarwa bayan tafiyar Buhari Belgium

Muna hanyar zuwa Kebbi daurin aure aka ce yan bindiga sun tare hanya, Shehu Sani

A wani labarin, tsohon Sanatan da ya wakilci Kaduna ta tsakiya a majalisar dokokin tarayya, Shehu Sani, ya bada labarin abin ya auku lokacin da suka dauki hanyar zuwa Kebbi halartan daurin aure.

Shehu Sani wanda ya shahara da yin jawaban barkwanci a kafafen ra'ayi da sada zumunta ya bayyana cewa an basu shawaran kawai suyi addu'a su cigaba da tafiyar.

Shi kuwa bai bi wannan shawara ba, addu'a dai ya yi amma ya juya motarsa ya koma gida.

Asali: Legit.ng

Online view pixel