Osinbajo ya jagoranci zaman majalisar zartarwa bayan lulawar Buhari Belgium

Osinbajo ya jagoranci zaman majalisar zartarwa bayan lulawar Buhari Belgium

  • Mataimakin shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo na jagorantar zaman majalisar zartarwa a fadar shugaban kasa
  • Hakan na zuwa ne a daidai lokacin da Shugaban kasa Muhammadu Buhari ke kasar Belgium domin halartan taron AU da EU
  • Manyan jami'an gwamnati da ministoci duk sun hallara a zaman majalisar wanda ke gudana a yau Laraba, 16 ga watan Fabrairu

Abuja - A yanzu haka, mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo na jagorantar zaman majalisar zartarwa a zauren fadar shugaban kasa da ke Abuja.

Osinbajo ya karbi ragamar majalisar ne yayin da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bar Abuja a ranar Talata, 15 ga watan Fabrairu, domin halartan taron kawancen Turai da Afrika a Brussels, kasar Belgium.

Osinbajo ya jagoranci zaman majalisar zartarwa a bayan idon Buhari
Osinbajo ya jagoranci zaman majalisar zartarwa a bayan idon Buhari Hoto: Buhari Sallau
Asali: Facebook

Wadanda suka halarci zaman na yau Laraba, 16 ga watan Fabrairu, sun hada da sakataren gwamnatin tarayya, Boss Mustapha; shugaban ma’aikatan gwamnati, Folashade Yemi-Esan, jaridar Daily Trust ta rahoto.

Kara karanta wannan

Da dumi-dumi: Shugaba Buhari zai shilla kasar Belgium halartar wani taro

Ministocin da suka halarci zaman sun hada da na jiragen sama, Hadi Siriki; na kudi, kasafi da tsare-tsaren kasa, Zainab Ahmed; na labarai da al’adu, Lai Mohammed, na kasuwanci da zuba jari, Niyi Adebayo; na sadarwa da tattalin arzikin zamani, Isa Pantami da na noma, Mohammed Abubakar.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Sauran sune karamin ministan harkokin waje, Zubairu Dada da karamin ministan kasafin kudi da tsare-tsare, Clem Agba.

Sauran ministocin sun halarci taron ne ta yanar gizo daga ofishoshinsu mabanbanta a Abuja.

Shugaba Buhari zai shilla kasar Belgium halartar wani taro

A baya mun kawo cewa Shugaban kasa Muhammadu Buhari zai bar Najeriya a yau dinnan zuwa kasar Belgium domin halartar wani taron shugabannin duniya.

Sanarwar da Legit.ng Hausa ta samo daga mai taimakawa Buhari a harkokin yada labarai ta ce, shugaban zai dawo Najeriya ranar Asabar idan Allah ya kaimu.

Kara karanta wannan

Pantami ya kaddamar da muhimmin aiki a mahaifar Shugaba Buhari

'Yan Najeriya da dama na nuna damuwa kan yadda Shugaba Buhari ke ci gaba da fita kasashen waje da sunan halartar taruka.

Asali: Legit.ng

Online view pixel