Yan bindiga sun kai farmaki gidan sarkin Hausawa a yankin Kaduna, sun sace mata da yara mata 4

Yan bindiga sun kai farmaki gidan sarkin Hausawa a yankin Kaduna, sun sace mata da yara mata 4

  • Yan bindiga sun kai hari gidan Sarkin Hausawan Anguwar Azara da ke Jere, hanyar babban titin Abuja zuwa Kaduna, Malam Ibrahim Tanko
  • Maharan sun yi awon gaba da matan sarkin da kuma yaransa mata su hudu
  • Hakazalika sun shiga gidan makwabcinsa inda suka sace wasu mutane hudu ciki harda mai jego

Kaduna - Yan bindiga sun farmakin gidan Sarkin Hausawan Anguwar Azara da ke Jere, hanyar babban titin Abuja zuwa Kaduna, Malam Ibrahim Tanko, inda suka yi garkuwa da matansa da yaransa mata su hudu.

Da yake tabbatar da lamarin ta wayar tarho, Tanko ya bayyana sunayen matansa da aka sace a matsayin Maimuna Ibrahim da Hauwawu Ibrahim.

Yan bindiga sun kai farmaki gidan sarkin Hausawa a yankin Kaduna, sun sace mata da yara mata 4
Yan bindiga sun kai farmaki gidan sarkin Hausawa a yankin Kaduna, sun sace mata da yara mata 4 Hoto: channelstv.com
Asali: UGC

Ya ce an saki uwargidarsa Hauwawu daga bisani bayan wadanda suka yi garkuwa da ita sun gano cewa tana da lalurar hawan jini.

Kara karanta wannan

Yan bindiga sun shafe tsawon kwanai 3 suna kai mamaya garuruwan wata jiha a arewa

Ya ce yan bindigar wadanda ke dauke da muggan makamai sun farmaki gidan nasa ne da misalin karfe 11:52 na daren ranar Talata.

Ya ce ya yi nasarar guduwa ne ta hanyar amfani da kofofin baya.

Tanko ya ce:

“Bayan sun dudduba basu ganni bane sai suka shiga dakin da yarana mata suke bacci sannan suka yi awon gaba da su.”

Sarkin Hausawan ya bayyana sunayen yaransa da aka sace a matsayin Aisha Ibrahim, Farida Ibrahim, Zainab Ibrahim da Hussaina Ibrahim.

A cewarsa, yan bindigar sun kuma shiga gidan wani makwabcinsa sannan suka yi awon gaba da mutane hudu ciki harda wata mai jego Laraba Umar.

Ya ce:

“A zahirin gaskiya sun yiwa mijin matar duka har sai da ya rasa inda kansa yake. Yanzu haka yana jinya a wani asibitin kudi a Katari.”

Kara karanta wannan

Yan bindigan sanye da kayan sojojin Najeriya sun bindige wani shahararren dan kasuwa har lahira

Ya kuma ce sojoji sun isa yankin awa daya bayan yan bindigar sun arce da mutanen.

Da aka tuntube shi, kakakin yan sandan jihar Kadunam, ASP Mohammed Jalige, ya ce yan sanda basu san da lamarin ba.

Ya yi alkawarin tuntubar kwamandan yan sandan Katari da yin karin bayani.

Jirgin yaki ya ragargaji 'yan ISWAP a Marte, sojoji da dama sun jikkata a Abadam

A wani labari na daban, mun ji cewa hare-haren bama-bamai ta sama da rundunar sojojin sama suka kai ya kashe yan ta’adda 34 a garin Marte da ke jihar Borno, PRNigeria ta rahoto.

Hakan na zuwa ne adaidai lokacin da sojojin kasa su tara suka jikkata a lokacin da ayarin motocinsu ya taka wani bam da yan ta’addan suka binne a karkashin kasa a Malam Fatori a karamar hukumar Abadam da ke jihar.

An tattaro cewa dakarun na kokarin kai hari kan mayakan ISWAP da ke Tumbun Dan Katsina lokacin da lamarin ya afku.

Kara karanta wannan

Yan bindiga sun hallaka mutum 10, sun sace Hakimi a jihar Katsina

Asali: Legit.ng

Online view pixel