Adashin N2,000 take kullum: Jami'ai kan mabaraciyar da aka kama da N500,000 da $100 a Abuja

Adashin N2,000 take kullum: Jami'ai kan mabaraciyar da aka kama da N500,000 da $100 a Abuja

  • Hukumomi a birnin tarayya Abuja sun shirya sakin mabaraciyar da aka kama kwanakin baya da makudan kudi
  • Hukumar ta bayyana cewa jami'an yan sanda sun kammala binciken da suke gudanarwa a kanta
  • An gano adashin dubu biyu take yi kulli yaumin tsawon lokaci

Abuja - Jami'ar hukumar birnin tarraya Abuja FCTA sun bayyana cewa mabaraciyar da aka kama da kudi N500,000 da $100, Hadiza Ibrahim ba mai laifi bace kamar yadda akayi zargi.

A cewar FCTA, binciken da aka gudanar ya nuna cewa Hadiza ba tada alaka da wasu yan kwaya, masu garkuwa da mutane, ko masu safarar makamai.

Jami'an sun bayyana cewa ta samu kudin ne ta hanyar yin adashin N2000 kullum.

Yayin hira da manema labarai ranar Alhamis a Abuja, Dirakan jin dadin al'umma na hukumar, Malam Sani Amar, ya ce an baiwa yan sanda lokacin aikinsu kuma sun tabbatar da cewa matar bata da alaka da wani mutanen banza.

Kara karanta wannan

Wahalar man fetur: N600 ake sayar da litan mai yanzu a Abuja

Amar yace:

"Mun fahimci Hadiza bata aikata wani laifi kuma idan ka duba kudin da ke hannunta, za ka ga tarasu tayi."
" Tana da wayau sosai yadda ta zabi wasu wurare na musamman don bara, inda take samun manyan kudade."

Abuja
Adashin N2,000 take kullum: Jami'ai kan mabaraciyar da aka kama da N500,000 da $100 a Abuja Hoto: Vanguard
Asali: Facebook

Sana'ar da Hadiza keyi kan ta fara bara

Yayin amsa tambayoyin manema labarai, Hadiza tace gabanin fara bara tufafi take sayarwa amma basusssuka sun yi mata yawa.

Ta ce sama da shekaru goma kenan tana bara.

Kama Hadiza

An kwamushe wata mabaraciya mai suna Hadiza Ibrahim a Abuja dauke da kudi N500,000 da kuma dala 100 kwanakin baya.

Jaridar Punch ta rahoto cewa mazauna yankin sun shiga rudani bayan da aka samu matar dauke da wadannan makudan kudade.

Kara karanta wannan

Kotu ta sa a yi wa matashin ɗan kasuwa Bulala Bakwai a jihar Kaduna

Kakakin hukumar kula da harkoki, zamantakewa da ci gaban babban birnin tarayya, Shaka Sunday, ya tabbatar da cewar matar na tsare a hannun hukumar a yankin Bwari.

Ya bayyana cewa har yanzu wacce ake zargin bata yi bayanin yadda aka yi ta samu makudan kudaden da aka samu a jikinta ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel