Birnin masoya mafi arha: Birnin Abuja ne na 23 a duniya don shakatawar soyayya

Birnin masoya mafi arha: Birnin Abuja ne na 23 a duniya don shakatawar soyayya

 • Wani kamfanin kasuwancin yanar gizo ya fitar da rahoton kasashen da suka fi araha ga masu son ganawar soyayya
 • Abuja, na daya daga cikin wadannan kasashe, kuma birnin na Abuja shi ne 23 daga jerin kasashe 56
 • Mun tattaro muku wasu goma na farko da aka ce su ne biranen da za ku iya cin duniyarku da tsinke

Picodi, wani kamfanin kasuwancin yanar gizo na duniya, ya ambaci Abuja a matsayin birni na 23 mafi arha inda masoya ka iya cin duniyarsu da tsinke a ganawar soyayya- daga cikin manyan birane 56 na cashewa ga masoya duniya.

A wallafarsa ta baya-bayan nan, dandalin ya kididdigi adadin kudin da ake bukata don rakashewa a manyan biranen duniya.

Birnin Abuja ne gaba-gaba
Birane mafi araha ga masoya: Birnin Abuja ne na 23 a duniya don shakatawar soyayya | Hoto: dailytrust.com
Asali: Depositphotos

Rahoton ya yi nazari kan manyan abubuwan da suka shafi rakashewa da suka hada da cin abincin dare a otal, kwalbar giya da tikitin shiga sinima, kamar yadda TheCable ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Ni ba zan kore ku ba: Gwamna Zulum ya gano Malamai 3800 ba su da abinci a koyarwa

A cewar bincike:

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

"Abincin dare na mutum biyu a gidan cin abinci na tsaka-tsaki tare da giya da kallon fim ya kai N33,500 ($81) a Abuja."

Kasashe 10 da masoya ka iya cin duniyaru da tsinke cikin sauki

A kasa ga jerin manyan birane 10 mafi arha domin ganawar masoya:

 1. Istanbul, Turkiyya - $44 (N18,300)
 2. Bogota, Colombia - $48 (N19,959)
 3. Buenos Aires, Argentina - $53 (N22,037)
 4. Belgrade, Serbia - $54 (N22,454)
 5. Lima, Peru - $55 (N22,870)
 6. Hanoi, Vietnam - $56 (N23,285)
 7. Kyiv, Ukraine - $56 (N23,285)
 8. Nur Sultan, Kazakhstan - $58 (N24,116)
 9. Minsk, Belarus - $58 (N24,116)
 10. Sao Paulo, Brazil - $60 (N24,949)

Ango ya barke da kuka wajen bikin aurensu saboda tuna mutuncin da Amarya tayi masa

A wani labarin, an samu wani mutumi da labarinsa ya karada shafukan sada zumunta na zamani saboda yadda ya rika kika a wajen bikin aurensa.

Kara karanta wannan

Yadda yan Najeriya ke kuka su zubda hawaye idan suka karbi tallafin N5,000, Sadiya Farouk

A wasu sakonni da ya fitar a shafinsa na Twitter kwanaki, Majekodunmi Abayomi ya bada labarin yadda matarsa ta taimaka masa.

Abayomi ya ce ya hadu da wannan mutumiyar kirki da ta zama matarsa ne a shekarar 2018. Kamar yadda Majekodunmi Abayomi ya fada, sa’ilin da ya fara haduwa da amaryar a, albashinta ya ribanya na sa kusan sau daya da rabi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel